Shugaba Buhari ya fada mana mu murkushe 'Yan Boko Haram inji sabon Hafsun Sojojin sama

Shugaba Buhari ya fada mana mu murkushe 'Yan Boko Haram inji sabon Hafsun Sojojin sama

- Shugaban kasa ya bukaci hafsun sojoji su murkushe ‘Yan ta’addan Boko Haram

- Muhammadu Buhari ya bada wannan umarnin ne ta bakin Janar Lucky Irabor

- Shugaba Buhari da Minista sun bukaci a samu hadi-kai tsakanin dakarun kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hafsoshin sojoji su dage wajen kawo karshen matsalar ta’addanci a yankin Arewa maso gabas.

Jaridar This Day ta ce shugaban Najeriyar ya bukaci sababbin shugabannin tsaron su murkushe ‘yan ta’addan Boko Haram ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban hafsun sojojin sama, Air Vice Marshal Oladayo Amao ya yi magana lokacin da ziyarci Maiduguri domin ya gana da dakarun da ke fagen daga.

Air Vice Marshal Oladayo Amao ya ce Mai girma shugaban kasa ya yi masu magana ne ta bakin shugaban hafsun tsaro na kasa, Manjo Janar Lucky Irabor.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun hallaka mutane 23 a Kaduna

Manjo Janar Lucky Irabor ya umarci sababbin hafsoshin su kawo sababbin dabaru da za su taimaka wajen ganin bayan ‘yan ta’addan da su ka addabi yankin.

Amao ya shaida wa dakarun sojojin saman Operation Lafiya Dole cewa shugaba Buhari ya na son ganin an samu zaman lafiya ta yadda abubuwa za su koma daidai.

Hafsun sojojin saman ya ce shugaban kasa da Ministan tsaron Najeriya sun bukaci sojojin sama su ba sojojin kasa hadin-kai wajen ganin an kawo zaman lafiya.

Air Vice Marshal Amao ya bayyana cewa ya gana da dakarun sojojin da ke yakin Boko Haram, daga ciki har da rundunar hadin-gwiwar MNJTF da Operation Lafiya Dole.

KU KARANTA: Dubun masu garkuwa da mutane da safarar mugayen makamai ta cika

Boko Haram: Abin da Shugaba Buhari ya fada mana – Sabon Hafsun Sojojin sama
Shugaba Buhari da sababbin Hafsun Sojoji Hoto: @NgrPresident
Asali: Twitter

Jami'in ya ce zai maida hankali wajen hare-haren hadin-giwa, horas da dakarun sojoji, samar da makamai masu lafiya da tarbiya da kuma jin dadi da walwalar sojoji.

A ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu, 2021 ne kuma ku ka ji cewa Shugaban kasar ya kare aikin dogon da gwamati za ta yi zuwa Jamhuriyar Nijar, wanda wasu ke suka.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin ginin layin dogon da zai ratsa Kano-Dutse-Jibiya har zuwa Maradi a jamhurriyar Nija mai tsayin kilomita 280.

Muhammadu Buhari ya ce jirgin kasan Kano-Katsina-Jibiya-Maradi zai bunkasa kasuwanci a Afrika.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel