N40bn da Gwamnatin Tarayya za ta ba ASUU zai jawo matsala inji Kungiyoyi

N40bn da Gwamnatin Tarayya za ta ba ASUU zai jawo matsala inji Kungiyoyi

- Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ba Jami’o’i N40bn a matsayin EA

- Kungiyoyin SSANU, NASU, da NAAT sun ce su ba ayi masu adalci ba

- Sauran Ma’aikata sun ce ba za a yarda ASUU kadai ta tashi da 75% ba

A ranar Laraba ma’aikatan jami’an gwamnatin Najeriya wadanda ba su koyarwa su ka gargadi gwamnati game da kudin da ta ke shirin biyan ASUU.

Kungiyoyin SSANU, NASU da NAAT na malaman fasaha da sauran ma’aikata jami’o’i su na kukan akwai rashin adalci wajen yadda za a raba wannan kudi.

Kafin ASUU ta janye yajin-aiki yau, sai da gwamnati ta yi alkawarin biyan jami’o’i Naira biliyan 40 a matsayin alawus din karin aikin da ake jibga masu.

A daidai lokacin da kungiyar ASUU ta bada sanarwar janye yajin-aiki, sai wadannan kungiyoyi su ka fito su na cewa an zalunce su sosai a kason da aka yi.

KU KARANTA: Yajin-aikin da mu ke yi ya zo karshe - ASUU

N40bn da Gwamnatin Tarayya za ta ba ASUU zai jawo matsala inji Kungiyoyi
Manyan 'Yan SSANU a zama Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto kungiyoyin uku su na kukan cewa kungiyar ASUU ta tashi da 75% na wannan kudi, yayin da aka bar dukkansu da 25% kacal.

Shugaban NAAT na kasa, Kwamred Ibeji Nwokoma, ya ce duk wanda ke tunanin cewa sauran ma’aikata za su koma aiki a wannan tsari ya na mafarki ne.

A cewar Nwokoma, su na neman ganin yadda za su zauna da gwamnati domin shawo kan lamarin.

Shi ma shugaban SSANU, Kwamred Mohammed Haruna Ibrahim, ya ce da wannan kaso, da alamu gwamnati ba ta neman ganin an zauna lafiya a jami’o’i.

KU KARANTA: ASUU ta fadi lokacin komawa aiki

Haruna Ibrahim ya ce dole sai dai a raba alawus din daidai wa-dai-da watau 50%-50%, domin 'yan kungiyar ASUU ba su fi sauran ma’aikatan jami'an yawa ba.

Dazu kun ji cewa Malaman Jami’a sun fadi dalilin su na hakura da yajin-aikin da ake yi tun watan Maris, su ke shirin bude makarantun gwamnatin kasar.

Kungiyar ASUU ta ce gwamnati ta fara cika alkawuranta, ta ce amma muddin shugaba Muhammadu Buhari ya saba alkawari, za su sake komawa yaji.

ASUU ta ce biyan EA ya na cikin dalilin dakatar da daya daga cikin yajin-aiki mafi tsawo,

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel