Satar kudi: Lauyan EFCC ya doke Patience Jonathan a kotu, an sa ranar zaman karshe

Satar kudi: Lauyan EFCC ya doke Patience Jonathan a kotu, an sa ranar zaman karshe

- EFCC ta koma kotu da mai dakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Alkali Chika Obiozor ya karbi sauraron shari’ar da ake yi tun shekarar 2017

- A watan Afrilu za a san ko kotu za ta karbe kudin asusun Patience Jonathan

Babban kotun tarayya da ke zama a Legas ta sa ranar 13 ga watan Afrilu a matsayin ranar sauraron shari’ar Dame Patience Jonathan da hukumar EFCC.

Channels TV ta rahoto cewa Alkali mai shari’a Chika Obiozor ya zabi wannan rana a jiya bayan ya tattauna da duka lauyoyin bangarorin da ake shari’a da su.

Hukumar EFCC ta na kokarin karbe wasu kudi Dala miliyan 5.8 da kuma Naira biliyan 2.4 daga hannun mai dakin tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan.

Chika Obiozor zai saurari wannan shari’a da aka fara tun a 2017, bayan gwamnatin tarayya ta nemi karbe dukiyar da ke asusun Patience Jonathan har abada.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Patience Jonathan

Alkali Mojisola Olatoregun ne ta fara sauraron wannan shari’a, amma sai yayi ritaya daga aiki a 2019.

Kafin mai shari’a Mojisola Olatoregun ya ajiye aiki, ta zartar da hukunci a soma rike dukiyar mai dakin tsohon shugaban kasar da aka samu a wasu bankuna biyu.

A zaman da aka yi ranar 8 ga watan Fubrairun 2021, lauyan EFCC, Abass Muhammad, ya yi wa Alkali bayanin yadda aka dauko wannan shari’a tun daga 2017.

Lauyoyin da ke kare Misis Jonathan; Kolawole Salami da Ige Asemudara, sun bukaci Alkali ya sake shari’ar daga farko tun da maganar ta dawo danya a gabansa.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta gana da Patience Jonathan a Aso Villa

Satar kudi: Lauyan EFCC ya doke Patience Jonathan a kotu, an sa ranar zaman karshe
Jonathan da mai dakinsa, Patience Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

Chika Obiozor bai amince da bukatar Dame Jonathan ba, ya bukaci a dakatar shari’ar zuwa 13 ga watan Afrilu, 2021 domin a ji ko za a karbe dukiyar na din-din-din.

A 2019 ne wata babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zaman ta a jihar Kano ta ba hukumar EFCC damar karbe dukiyar da ke hannun matar tsohon shugaban kasar.

Kotun ta ba EFCC izinin wucin gadi na karbe wannan kudin. Alkali ya kuma bukaci a sanya kudin a asusun bai daya na gwamnatin tarayya wanda ke bankin CBN.

Idan Patience Jonathan ta rasa wannan shari'a, kudin na ta za su koma hannun gwamnati har abada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel