Ku shirya jure tsadar man fetur, Ministan mai ga 'yan Najeriya

Ku shirya jure tsadar man fetur, Ministan mai ga 'yan Najeriya

- Karamin ministan man fetur ya gargadi 'yan Najeriya da su shirya jure wahalar fetur

- Ya bayyana cewa, farashin man fetur ya haura, don haka dole a jure wahalar sa

- Ya kuma bayyana cewa a yanzu kowacce ganga daya ta haura kusan dala 60

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva ya gargadi ‘yan Nijeriya da su kasance cikin shirin jure wahalar karin farashin mai yayin da farashin danyen mai ya haura sama da $60 a kowace ganga, Vangaurd News ta ruwaito.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin Inganta Kudin Najeriyar a ranar Talata, Sylva ya ce ba tare da samar da tallafi a cikin kasafin kudin 2021 ba, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), ba zai iya ci gaba da daukar nauyin da ke kasa-kasa ba.

A halin yanzu, farashin man fetur ya kai N160 zuwa N165, farashin da aka sanya lokacin da danyen ya yi sama da $43 a kowace ganga, watanni hudu da suka gabata.

KU KARANTA: Cin hanci da rashawa na hau-hawa ne saboda ba a daure masu laifi, in ji Amaechi

Ku shirya jure tsadar man fetur, wani minista ya fada wa 'yan Najeriya
Ku shirya jure tsadar man fetur, wani minista ya fada wa 'yan Najeriya Hoto: International Centre for Investigative Reporting
Asali: UGC

A cewar Ministan, yayin da kudaden shigar da gwamnati ke samu ya inganta ta hanyar hauhawar farashin danyen mai, ba za a iya damunta cikin biyan tallafi ba.

Ya ce: “Tunda muna inganta komai, NNPC na bukatar kuma tayi tunani game da inganta farashin kayan saboda kamar yadda kowa ya sani farashin mai yana inda yake a yau, $60.

"A matsayinmu na kasa, bari mu dauki fa'idar karin farashin danyen mai kuma ina fatan za mu kasance a shirye mu dauki dan karamin ciwo a kan karin farashin kayayyakin", in ji shi.

KU KARANTA: Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC kan zaben 2023 mai zuwa

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta kashe jimillar Naira biliyan 37 a kan shirin tallafawa 'yan Najeriya da aka fi sani da Survival Fund, in ji Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, Nigeria Tribune ta ruwaito.

Kudin, kamar yadda ya sanar, an kashe su ne kan wasu tsare-tsare kamar N50,000 ga masu aiki a ma'aikatu na tsawon watanni uku zuwa sama da aka rabawa mutane 300,000.

An kuma tallafawa wasu masu sana'ar hannu da N30,000 kusan mutum 100,000, da rajistar sunan kasuwanci a CAC na mutane 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta biya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.