Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC kan zaben 2023 mai zuwa

Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC kan zaben 2023 mai zuwa

- Sabon rikici ya barke a jam'iyyar APC a kokarin sabon tsarin rajistar dake gudana a jam'iyyar

- Masana na bayyana cewa, Tinubu ya nuna alamun harin kujerar shugaban Najeriya a 2023

- Sai dai, zuwa yanzu shi Tinubu bai fito ya nuna kwadayinsa ga kujerar shugabancin kasar ba

Wani sabon rikici ya tunkaro jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, sakamakon wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin babban jigo a jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu, BBC Hausa ta ruwaito.

Shi dai Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya ce aikin sabunta rijistar 'yan jam'iyyar dake gudana yanzu haka a jihohin Najeriya bashi da wani tasiri.

''Sabunta rajistar da jam`iyyar ke yi tamkar a sanya daya ne kana kuma cire daya, don haka ni ina ganin ba wata karuwa bace" a cewar Tinubu.

Hasashe ya nuna cewa, Tinubu bai ji dadin yadda jam'iyyar ta sauya tsarin jaddada rajistar ba.

KU KARANTA: Sabon shugaban sojoji ya sake ziyartar jihar Borno a karo na biyu

Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC kan zaben 2023 mai zuwa
Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC kan zaben 2023 mai zuwa Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Alhaji Maikano Zara, wani dan jam'iyyar ne mai rin wannan ra'ayin, da yace ''Bazai goyi bayan sabunta rijistar yan jam'iyyar bane saboda yaga cewa bukatunsa basu biya ba, ya fi son a tsaya daga kauri sai guiwa''

Sai dai wasu makusantan Bola Tinubu na cewa ba a fahimce shi ba ne, kuma babu yadda yin rajistar za ta shafi karfin iko da fada a jinsa a jam'iyyar APC.

Alhaji Ibrahim Masari, wani jigo a jam'iyyar ta APC a Najeriya, wanda yace ''Abin da yake magana shine a inganta katin da ake da shi na baya wanda aka samar ta yanar gizo, sai a daura a kai ba wai a sake yin wani ba''.

Alhaji Ibrahim masari shima yana kan ra'ayin cewa gudanar da rajistar bashi da wani amfani ko tasiri ga mabiya jam'iyyar.

''Sake rijistar jam'iyya ba zai canja komai ba, sannan bazai rage tasirin mai tasiri ba in har yana da tasirin'', a cewar Masari.

Sai dai masana, irin su Mallam Kabiru Sufi na kwalejin share fagen shiga jami'a ta jihar Kano na cewa irin wadannan kalamai daga bakin Bola Tinubu a matsayinsa na jagora, na nuni da cewa akwai baraka a jami'iyyar.

A nasa bangaren, Tinubu bai fito fili ya nuna sha'awarsa ga mulkar Najeriya ba.

KU KARANTA: Shirin ciyar da yara 'yan makaranta ya samar da ayyuka 14,000 a Neja, Jami'i

A wani labarin, Shugaban majalisar dattijai, Yahaya Abdullahi, ya ce zauren dattijai zai tattauna kan matsalar rikicin makiyaya Fulani a duk fadin kasar a ranar Talata, jaridar Punch ta ruwaito.

Abdullahi, wanda ya zanta da manema labarai a ofishinsa, ya ce mataimakinsa wanda ke wakiltar Ondo ta Arewa a Majalisar Dattawa, Farfesa Ajayi Boroffice, zai gabatar da kudiri kan batun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel