Oyegun: Tsohon shugaban APC ya ki amincewa da ra'ayin su Tinubu, ya fadi muhimmanci sabunta rijista

Oyegun: Tsohon shugaban APC ya ki amincewa da ra'ayin su Tinubu, ya fadi muhimmanci sabunta rijista

- Cif John Odigie-Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC, ya ki amincewa da ra'ayin Tinubu da Akande akan sabunta rijista

- Dattijo a APC, Bisi Akande, ya soki aikin sabunta rijistar mambobin jam'iyyar da shugabanci riko a karkashin Mai Mala Buni

- A yayin da ya ke karbar sabuwar rijitarsa a ranar Asabar, Tinubu ya bayyana cewa yana goyon bayan ra'ayin Akande

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Chief John Odigie-Oyegun, ya ƙaryata cece kucen da ke yawo kan sabunta wa da yin sabuwar rejistar jam'iyyar da ke kan gudana yanzu, karkashin kwamitin gudanarwar jam'iyyar na rikon kwarya bisa jagorancin Gwamna Mai Mala Buni.

Odigie-Oyegun ya bayyana wannan rejista a matsayin abun da ya zama dole domin wanke jam'iyyar daga duk wani datti, da kuma bai wa sabbin jini damar taka rawar da ya dace.

Ya zanta ne da jaridar PUNCH a wata tattaunawa da suka yi da shi ta wayar tarho daga Benin, a ranar Juma'a.

Odigie-Oyegun ya yi magana ne kasa da awanni 48 bayan da pINC na jam'iyyar, Chief Bisi Akande, ya caccaki shirin rejistar, da cewar aikin banza ne, ba zai yi wani tasiri wajen ci gaban jam'iyyar ba.

KARANTA: Rijista: An tashi baran-baran ba shiri bayan rikici ya barke yayin taron shugabannin APC

Akande ya musanya hakan yana mai cewa, "Babu wani shirin kidaya da aka gudanar a kasa da shekaru goma kuma ba a sake yin rejistar masu zabe a kowanne zabe.

Oyegun: Tsohon shugaban APC ya ki amincewa da ra'ayin su Tinubu, ya fadi muhimmanci sabunta rijista
Oyegun: Tsohon shugaban APC ya ki amincewa da ra'ayin su Tinubu, ya fadi muhimmanci sabunta rijista
Source: UGC

"Idan muka kalli wannan kawai, zan ce wannan sabuntawa da yin sabuwar rejista kasa da shekaru goma da yin waccan rejistar, kamar almubazzaranci ne da kuma nuna rashin ilimin shugabanci na shuwagabannin rikon jam'iyyar a yanzu.

"Kuma wannan alama ce ta nuna cewa ba a san inda ya kamata a yi amfani da kudaden jam'iyyar ba, musamman ma yanzu da ake fama da karyewar tattalin arziki a kasar.

KARANTA: An kama matasan da ke dillancin hotuna da bidiyon tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo

"Duk abubuwan da za a gudanar yanzu, sai dai a ci albarkacin waccan rejistar da aka yi a ranar 15 ga watan Fabreru 2014, da kuma N1bn da aka kashe a shekarar 2014, lokacin ma da ita kanta jam'iyyar ba ta da kudaden kanta na gudanar da ayyukan ta."

Sai dai, Odigie-Oyegun, yayin da ya ke goyon bayan hukuncin kwamitin Gwamna Buni, ya ce "Mutane da yawa sun shiga cikin jam'iyyar, wasu sun samu mukamai wasu kuma sun rasa. Wannan ya sa dole mu san su waye ya'yan jam'iyyar APC domin gujewa fadawa yanayin da aka shiga a lokacin baya."

Da aka tambaye shi ko ya yi tsokacin ne biyo bayan kalaman Akande, Odigie-Oyegun ya ce, "Ba za ka iya yin amfani da rejistar jam'iyya wajen cin zabe ba. Mutanen kasar nan, kaso 95 wadanda ba mambobin jam'iyyu ba ne, su ne dai ke tantance wanda zai shugabance su, ba wai mambobin jam'iyyu ba.

"Idan har ka sanya adadin mambobin jam'iyar mu, ba su wuce mutane miliyan 12 ba. Lallai ke nan, kwamitin rikon na da madogara kan gudanar da wannan shiri na yin rejistar da sabunta wa, ya kamata mu basu goyon baya da kwarin guiwa. Ni ban ga wani aibu a rejistar ba."

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel