Rikicin APC: Za a sasanta Mataimakin Shugaban Majalisa da Ministan Buhari

Rikicin APC: Za a sasanta Mataimakin Shugaban Majalisa da Ministan Buhari

- Jagororin jam’iyyar APC za su dinke barakar cikin gidan da ke jihar Delta

- Olorogun O’tega Emerhor shi ne zai jagoranci sulhun cikin gidan da za ayi

- O’tega Emerhor ya ce sabanin da aka samu ya jawo wa APC a zaben 2019

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Delta ta fara kokarin sasanta wasu jagorinta da ke rikici, Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu.

Jaridar ta ce wasu ‘yan cikin gidan APC sun shaida mata cewa za a tura manyan wakilai da za su zauna da Ovie Omo-Agege; Festus Keyamo da Great Ogboru.

Ana samun rashin jituwa tsakanin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, Ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo SAN.

Rahoton ya ce za kuma a zauna da babban kusan jam’iyyar APC a jihar Delta, Cif Great Ogboru.

KU KARANTA: PDP ta yi magana game da ganawar Femi Fani Kayode da APC

Punch ta ce wanda zai jagoranci wannan zama na sulhu shi ne tsohon ‘dan takarar gwamnan jihar Delta a karkashin jam’iyyar Olorogun O’tega Emerhor.

Olorogun O’tega Emerhor ya bayyana haka bayan shi da mai dakinsa Rita Olorogun Emerhor sun sabunta rajistarsu na jam’iyyar APC a Evwreni, garin Ughelli.

Mista Olorogun Emerhor ya ce: “Rikicin cikin gidan da ya barko wa jam’iyyar mu daf da kuma bayan zaben 2019, ya taimaka wa PDP mai mulki a Delta.”

“Daf da 2019, mun bude kofar jam’iyyarmu domin sabon-shiga su zo cikinmu. A lokacin ne wani gungu na Ovie Omo-Agege da Great Ogboru su ka shigo mana.”

Rikicin APC: Za a sasanta Mataimakin Shugaban Majalisa da Ministan Buhari
Omo Agege da Festus Keyamo Hoto: www.thenewsnigeria.com.ng
Source: UGC

KU KARANTA: Ministan sufuri ya kai sabuwar Jami’a zuwa Mahaifarsa

“Kun san a siyasa ana samun sabani. Lokacin da su ka zo, sai mu ka rasa alkibla. A wannan rikici sai jam’iyyar ta barke biyu, aka yi zabe, har aka je kotun koli.”

Lokaci ya yi da APC za ta birne banbancin sabanin da ke cikin gidanta, a cewar Olorogun Emerhor.

A baya kun ji cewa wasu tsofaffin ‘Yan Buhariyya sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin hallaci a kasar Yarbawa wajen yin nadin mukamai.

Wadannan mutane na-kusa da Buhari sun fito su na kuka, sun ce an manta da duk gudumuwarsu.

Lekan Yusuf na kungiyar Buhari Youth Organisation a jihar Legas ya ce akwai tsofaffin ‘yan CPC wanda aka manta da wahalar su ka sha bayan an dare kan mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel