Wasu Magoya baya sun ce an bar su da hayaki bayan motar Buhari ta tashi

Wasu Magoya baya sun ce an bar su da hayaki bayan motar Buhari ta tashi

- Magoya bayan Shugaban kasa sun fito, sun yi babatu a fili bayan an raba kujeru

- Wasu ‘Yan siyasa sun ce ba a yin rabon mukamai da kyau a gwamnatin Buhari

- Su na zargin shugaba Buhari da watsi da ‘yan bangaren CPC wajen bada kujeru

Wasu daga cikin wadanda su ke tare da shugaba Muhammadu Buhari tun ya na jam’iyyar CPC a kudu maso yamma sun ce ana rabon mukamai ta bai-bai.

Jaridar Vanguard ta rahoto wadannan ‘yan siyasa su na cewa ba ayi wa 'yan yankinsu adalci wajen rabon mukamai da gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi.

Magoya bayan su ka ce an yi rabon mukamai ba tare da an hada da wadanda su ka yi wa Buhari bauta tun a lokacin tafiyar CPC da zabukan 2015 da 2019 ba.

Su dai wadannan mutane su na ganin cewa a matsayinsu na kwararru a wajen aikinsu, kuma wadanda su ka ba Buhari goyon baya, ya kamata a ba su mukamai.

KU KARANTA: Lauya ya na so a matsawa Buhari ya nada sabon IGP

Adeyemi Idowu ya ce ya san mutanen CPC da yawa da ba ayi wa sakayya wajen rabon mukamai ba, sai dai aka yi ta zakulo ‘yan bangaren tsohon barin ACN.

Idowu ya ce daga cikin irin wadannan ‘yan siyasa akwai: Hon. Lanre Kuku, Fatai Olatunji; Olufemi Olaore, Hammed Elegbeleye daga jihohin Ogun da kuma Oyo.

Sai irinsu: Wole Adunola, Kola Olabisi a Osun; Adewale Agboola Dixon, Owa Babatunde a Ekiti, Soji Ehinlanwo, Damilola Oluyemi da Hamisu Mohammed a Ondo.

Lekan Yusuf na kungiyar Buhari Youth Organisation a Legas ya ce akwai tsofaffin ‘yan CPC wanda aka manta da wahalar su ka sha bayan an dare kan mulki.

KU KARANTA: Amaechi: Gwamnatin Buhari za ta gina sabuwar Jami’a a Ribas

Wasu Magoya baya sun ce an bar su da hayaki bayan motar Buhari ta tashi
Buhari wajen kamfe a Jigawa Hoto: @APCNigeria
Asali: Twitter

Yusuf ya ce Buhari ya manta da irin gudumuwar da Thomas Adu, Olufemi Adeniregun, Blessing Okere, Cif Emi Abata Balogun, da Abayomi Nurain su ka ba shi.

Wadannan ‘yan siyasa sun fara kuka ne bayan shugaban kasar ya zabi tsofaffin hafsun sojojin Najeriya cikin wadanda za a ba kujerun Jakadun kasashen waje.

Bayan mako guda da yi ma ritaya, shugaban kasa ya aikawa Sanatoci sunayen Tukur Buratai, Olonisakin, Ibok-Ete Ibas da Abubakar Sadique domin ba su mukamai.

Muhammadu Buhari ya kara sunayensu a cikin wadanda zai nada Jakadu zzuwa kasashen waje.

Jam’iyyar PDP ba ta goyon bayan a ba tsofaffin hafsoshin mukaman Jakadu. Har ma PDP ta roki Sanatoci su ki yin na’am da wannan shiri da gwamnati ta ke yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel