Ko a jikinmu: PDP ta ce bata damu da ganawar da Fani-Kayode yayi da shugabannin APC ba

Ko a jikinmu: PDP ta ce bata damu da ganawar da Fani-Kayode yayi da shugabannin APC ba

- PDP ta ce har yanzu ba ta samu wani rahoto a hukumance game da yiwuwar sauya shekar Femi Fani-Kayode ba

- Jam’iyyar adawar ta ce duk da cewar FFK ya hadu da wasu shugabannin APC, sam bata damu da lamarin ba

- A ranar Litinin din da ta gabata, tsohon ministan ya haifar da rudani bayan ganawa da yayi da Yahaya Bello da Mai Mala Buni, wadanda dukkansu gwamnonin APC ne

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Ribas ta mayar da martani game da ganawar da tsohon minista Femi Fani-Kayode ya yi da wasu shugabannin jam’iyyar All Progressives Congres (APC) mai mulki.

Da yake magana da jaridar The Punch, sakataren yada labarai na PDP a Ribas, Sydney Tambari, a ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu, ya ce tsohon ministan jirgin saman na da damar sauya sheka.

Tambari ya ce Fani-Kayode na da 'yancin yin hulda da kowa, don haka dalilin sauya shekarsa ba zai zo a matsayin abun mamaki ba.

Ko a jikinmu: PDP ta ce bata damu da ganawar da Fani-Kayode yayi da shugabannin APC ba
Ko a jikinmu: PDP ta ce bata damu da ganawar da Fani-Kayode yayi da shugabannin APC ba Hoto: @realFFK
Asali: Twitter

Ya kuma ce, ministan bai gabatarwa da shugabancin jam'iyyar na kasa takardar ficewarsa daga PDP ba a hukumance.

KU KARANTA KUMA: Ayarin motocin Zulum sun yi hatsari, mutum 2 sun rasa rayukansu

Idan za a iya tunawa Fani-Kayode a ranar Litinin, 8 ga watan Fabrairu, ya gana da wasu shugabannin APC da suka hada da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe.

Tuni ganawar ta haifar da gagarumin martani inda mutane da yawa ke bayyana cewa tsohon ministan na shirin komawa ga jam'iyya mai mulki.

Amma PDP reshen Ribas ta ce ba ta damu da jita-jitar ficewar FFK ba, tana mai cewa jam'iyyar adawar ta rasa "shugabanni da yawa" a hannun APC.

“A matsayinmu na jam’iyya, muna da shugabanni da yawa. Fani-Kayode mutum ne daya da muke girmamawa a matsayinsa na mai ruwa da tsaki amma kuma yana da 'yancin haduwa da duk wanda yake so ya ziyarta ko kuma halartar aikin duk wanda yake so ya halarta.

"Wannan baya damun mu a matsayinmu na jam'iyya saboda a yanzu ba mu samu wani rahoto a hukumance ba cewa zai sauya ko ya sauya sheka ba."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: 'Yan bindiga sun sace hadimin mataimakin gwamnan Taraba

A baya mun ji cewa DG na kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC (PGF), Salihu Lukman, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai amince da shigowar Femi Fani-Kayode cikin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba idan dan siyasar ya yanke shawarar komawa jam'iyyar.

PGF kungiya ce ta dukkanin gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC.

A cewar jaridar The Punch, babban daraktan kungiyar a cikin wata sanarwa ya ce rahotannin da ke nuna cewa Fani-Kayode, tsohon minista, na iya dawowa APC yana rikita tunani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel