‘Yan kwangilar da za su yi titin jirgi zuwa Maradi za su gina Jami’a a Najeriya
- Kamfanin kasar Portugal, Mota Engil zai gina wata Jami’a a Jihar Ribas
- Ministan sufuri ya ce kamfanin zai yi wannan aiki ne ba tare da an biya ba
- Wannan kamfanin ne aka ba kwangilar titin dogo daga Kano zuwa Nijar
A ranar Litinin, 8 ga watan Fubrairu, 2021, babban Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi, ya sanar da cewa za a samu karin wata jami’a a Najeriya.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ‘yan kwangilar da za su yi aikin titin dogon jirgin kasa daga Kano zuwa kasar Maradi ne za su gina wannan jami’a.
Mai girma Ministan ya bayyana cewa za a gina wannan jami’a ne a garinsa. Rotimi Amaechi ya sanar da wannan a shafinsa na Twitter, @ChibuikeAmaechi.
“Ko da ma can mu na da jami’ar sufuri da ake gina wa a Daura (Katsina). Saboda haka, mu ka yanke cewa kamfanin kasar Portugal da aka ba kwangilar dogon Kano zuwa Maradi, Mota Engil, zai gina babbar jami’a a jihar Ribas.” Inji Amaechi a Twitter.
KU KARANTA: Mun gano danyen mai a Arewa, an fara aikin hake-hake inji Minista
Amaechi ya ce za a rika koyar da ilmai dabam-dabam a wannan jami’a, akasin wanda ta ke Daura.
A cewar Ministan sufurin kasar, kamar yadda aka saba yi a wurare, “Wannan aiki ya na cikin gudumuwar da ‘yan kwangilar za su bada domin cigaban Najeriya."
Bayan haka, Ministan ya bayyana cewa za a tura mutanen kasar nan 300 da za su je kasar Portugal domin su yi kwas na musamman a harkar fasahar ginin dogo.
Mai girma Ministan ya ce a shekarar 2019 gwamnati ta yi haka, inda aka zabi wasu mutane 300 da aka tura zuwa kasar Sin domin a ba su horo a kan wannan fasaha.
KU KARANTA: Patience Jonathan za ta san matsayar dukiyarta a Kotu
Wani Bawan Allah ya caccaki Ministan a shafin Twitter, ya ce ayyukan da wadannan ‘yan kwangilolin su ke yi, ya nuna an yi rashin gaskiya wajen bada aikin.
Idan ku na biye da mu, za ku tuna cewa 'yan jarida sun yi wa Ministan sufurin kasa, Rotimi Ameachi, tambaya kan siyasar 2023, inda ake ganin zai nemi takara.
Rotimi Ameachi yace ba siyasa ke gabansa ba, kuma bai san wanda zai zama shugaban kasa ba.
Ana rade-radin cewa tsohon gwamnan na Ribas ya na cikin masu harijn kujera a 2023 a jam'iyyar APC, amma 'dan siyasar ya ce sam ba wannan ne gabansa ba a yanzu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng