Gwamnatin Buhari ta kashe N37bn a tallafin 'Survival Fund', in ji Osinbajo

Gwamnatin Buhari ta kashe N37bn a tallafin 'Survival Fund', in ji Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa ya bayyana adadin kudaden da gwamnati ta kashe a shirin Survival Fund

- Hakazalika babban banki ya fidda rahoton kudin da ya kashe a shirin Targeted Credit Facility

- Babban bankin ya kuma bayyana adadin da zai kara kashewa a shirin na Targeted Credit Facility

Gwamnatin Tarayya ta kashe jimillar Naira biliyan 37 a kan shirin tallafawa 'yan Najeriya da aka fi sani da Survival Fund, in ji Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, Nigeria Tribune ta ruwaito.

Kudin, kamar yadda ya sanar, an kashe su ne kan wasu tsare-tsare kamar N50,000 ga masu aiki a ma'aikatu na tsawon watanni uku zuwa sama da aka rabawa mutane 300,000.

An kuma tallafawa wasu masu sana'ar hannu da N30,000 kusan mutum 100,000, da rajistar sunan kasuwanci a CAC na mutane 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta biya.

KU KARANTA: Kungiyoyin Arewa suna marawa Gumi baya kan samar da filayen kiwo ta kasa

Gwamnatin Buhari ta kashe N37bn a tallafin 'Survival Fund', in ji Osinbajo
Gwamnatin Buhari ta kashe N37bn a tallafin 'Survival Fund', in ji Osinbajo Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya fitar a ranar Litinin ta bayyana cewa shirin na Survival Fund wani bangare ne a karkashin shirin nan na dorewar tattalin arziki (ESP) na gwamnatin Muhammadu Buhari.

Ya kuma bayyana cewa shirin wani yunkuri ne na magance mummunar tasirin barkewar COVID 19 akan 'yan Najeriya.

A cewar sanarwar, ministoci da shugabannin hukumomin sun kasance suna bayar da rahoton ci gaban da aka samu a aiwatar da ESP kamar yadda Osinbajo ya jagoranci taron kwamitin dorewar tattalin arziki a ranar Litinin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A wani rahoton babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayyana cewa bankin ya bada kudi a karkashin shirin da ake kira TargetdbCredit Facility da ya kai N192bn, kuma mutane da kamfanoni sama 426,000 ne suka ci gajiyar shirin.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa akwai karin da za a bayar na sama N100bn a karkashin shirin na Targeted Credit Facility.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa za ta tattauna kan rikicin makiyaya Fulani ranar Talata

A wani labarin, Mista Umar Ndashacba, Manajan Shirye-shirye na Shirin Ciyar da Makarantun Gida na Kasa (NHGSFP) a Neja, ya ce aƙalla an samar da ayyuka sama da 14,000 a cikin shekaru biyu da kasancewar shirin a jihar.

Ndashacba ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel