Tirkashi: 'Yan daba sun sake tarwatsa wani taron APC a Kwara, sun lalata motoci

Tirkashi: 'Yan daba sun sake tarwatsa wani taron APC a Kwara, sun lalata motoci

- 'Yan daba sun sake tarwatsa wani taron jam'iyyar APC a jihar Kwara sannan suka lalata motoci

- Da isan yan daban wajen taron, kai tsaye sai suka tunkari wajen da shugabannin jam'iyyar suka zauna don far masu

- Lamarin na zuwa ne kimanin kwanaki biyar bayan makamancin hakan ya faru a wani taron jam'iyyar mai mulki

Kimanin kwanaki biyar bayan ‘yan daba sun tarwatsa taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, an kai sabon hari kan magoya bayan jam’iyyar a karamar hukumar Edu na jihar, lamarin da ya kai ga kawo karshen taron a ranar Litinin.

An kira taron na ranar Litinin ne don kammala shirye-shiryen yin rajistar mambobin jam’iyyar na ranar Talata, jaridar Punch ta ruwaito.

Ku tuna cewa a ranar Laraba da ta gabata, rikici ya barke a irin wannan taron na masu ruwa da tsaki na APC a dakin taro na Banquet da ke gidan gwamnati, Ilorin inda sama da mutane 10 suka samu munanan raunuka.

Tirkashi: 'Yan daba sun sake tarwatsa wani taron APC a Kwara, sun lalata motoci
Tirkashi: 'Yan daba sun sake tarwatsa wani taron APC a Kwara, sun lalata motoci Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: 2023: Ministan Buhari ya yi alfahari, ya ce APC na da abin da za ta rike don ci gaba da shugabancin kasar

Rikicin baya-bayan nan ya barke ne a taron masu ruwa da tsaki da aka ce tsoffin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC ne suka shirya shi don wayar da kan mambobinsu kan shirin rijistan da ke gudana.

An tattaro cewa; taron wanda aka fara cikin kwanciyar hankali, ya zama rikici lokacin da wasu da ake zargin 'yan daba ne suka far ma wurin taron.

A yayin tattaunawar, an kai hari ga masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da ke wurin sannan aka lalata motocin wasun su.

Da yake magana da manema labarai a Ilorin bayan lamarin, daya daga cikin shugabannin APC da suka ga tashin hankalin, Umar Shaaba, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana abin da ya faru a matsayin maimaicin abunda ya faru a Ilorin.

A cewarsa, wasu 'yan iska sun kai hari wurin taron sannan kai tsaye suka tunkari shugabannin jam'iyyar da ke zaune.

Ya bukaci hukumomin tsaro da su zakulo wadanda suka tayar da rikicin tare da hukunta su.

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban Sakataren labaransa, Rafiu Ajakaye, ya ce;

“Gwamnatin ba ta daukar tashin hankali. Abun ya wakana a Edu ba abun yarda banne ko kadan. Duk wanda aka samu da hannu wajen tayar da hankali ya kamata a kamo shi sannan a hukunta shi. Gwamnan ya tausaya wa wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu ko suka samu rauni. Wannan baa bun yarda bane ko kadan.”

KU KARANTA KUMA: Hadiman Buhari da Ganduje sun fusata game da ikirarin komawar Fani-Kayode APC

Sanarwar ta kuma ambato gwamnan yana gargadin mutanen jihar game da yada labaran karya saboda illolin da yake haifarwa ga zaman lafiya da tsaron jihar.

Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su yi amfani da damar shirin rajistar.

A gefe guda, mun ji a baya cewa an ba jiga-jigan APC biyar wadanda suka ji munanan raunuka a rikicin da ya barke a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar reshen jihar Kwara gado a asibiti.

Suna samun kulawar likitoci a wasu asibitoci da ba a bayyana ba a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara, jaridar This Day ta ruwaito.

Shugaban jam’iyyar, Bashir Bolarinwa, wanda ya ziyarce su ya nuna farin ciki na ganin cewa suna samun lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel