Dalilin da ya sa Shugaba Buhari ba zai taba barin Fani-Kayode ya koma APC ba, jigon jam’iyya
- DG na kungiyar PGF, Salihu Lukman, ya yi martani ga ziyarar da Fani-Kayode ya kai wa wasu shugabannin APC kwanan nan
- Lukman ya bayyana dalilin da yasa duk wani yunkuri na gayyatar tsohon ministan zuwa jam’iyyar ba zai haifar da ‘da mai ido ba
- Jami’in ya ce sunan Fani-Kayode bai dace da APC ba
Babban darakta (DG) na kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC (PGF), Salihu Lukman, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai amince da shigowar Femi Fani-Kayode cikin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba idan dan siyasar ya yanke shawarar komawa jam'iyyar.
PGF kungiya ce ta dukkanin gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC.
A cewar jaridar The Punch, babban daraktan kungiyar a cikin wata sanarwa ya ce rahotannin da ke nuna cewa Fani-Kayode, tsohon minista, na iya dawowa APC yana rikita tunani.
KU KARANTA KUMA: Hadiman Buhari da Ganduje sun fusata game da ikirarin komawar Fani-Kayode APC
Lukman ya bayyana cewa tsohon ministan ya yi kaurin suna wajen yin maganganun batanci game da shugabannin APC da shugaban kasa.
DG din ya caccaki wasu shugabannin jam'iyyar kan ganawa da Fani-Kayode.
Ya ce:
"Ta yaya za a ba mutumin da a kwanan nan, idan ba' yan awanni da suka gabata ba ya rubuta wa ɗaya daga cikin shugabanninmu wasika a wulakance sannan ya yi Allah-wadai da kudirin siyasarsa na son zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu irin wannan gagarumar liyafar?
“Idan muka ce budaddiyar wasikar da ya rubuta zuwa ga babban jigonmu na kasa, wanda ya mamaye kafafen yada labaranmu a lokacin irin wannan liyafar, ba laifi ba ne, toh ya abun yake game da budaddiyar wasikar da ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar da ta gabata?"
A cewar Jaridar The Nation, shugaban PGF din ya lura cewa karrama tsohon ministan da shugabannin APC suka yi daidai yake da karrama halayyar cin mutunci.
KU KARANTA KUMA: Tirkashi: 'Yan daba sun sake tarwatsa wani taron APC a Kwara, sun lalata motoci
Ya yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na karɓar ɗan siyasan a cikin APC zai raunana yardar mambobin jam’iyyar fiye da tunani.
A gefe guda, Femi Fani Kayode ya ce ya gana da shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ne domin tattaunawa kan "halin da kasa ke ciki da harkokin siyasa da matakan da za a dauka don cigaba."
A sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter a ranar Talata, Fani-Kayode ya ce taron da suka yi na sada zumunci ne da hada hannu domin ceto Nigeria daga tsindumawa cikin yakin basasa.
Ya ce baya ga shugabannin na jam'iyyar APC, yana ganawa da shugabannin wasu jam'iyyun siyasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng