Sabon shugaban sojoji ya sake ziyartar jihar Borno a karo na biyu

Sabon shugaban sojoji ya sake ziyartar jihar Borno a karo na biyu

- Shugaban sojojin Najeriya a karo na biyu ya sake kai ziyara jihar Borno a arewa maso gabas

- Shugaban sojojin an bayyana zuwansa shi kadai sabanin ziyarar baya da ya je da sauran hafsoshi

- Ziyarar ta sa tana da nasaba da kokarin hada kan masu ruwa da tsaki don magance tsaro a yankin

Gabanin tabbatarwarsa da majalisar kasa, sabon shugaban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya ziyarci wasu rundunonin sojoji a jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban sojojin, wanda ya iso da safiyar ranar Litinin, ya samu rakiyar jami’ai daga OPL Lafiya Dole da runduna ta 7 zuwa hedikwatar rundunar kafin ya ci gaba da zuwa wasu wuraren.

Janar Attahiru, wanda ya karbi aiki daga hannun Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai makonni biyu da suka gabata, ya sake dawowa Maiduguri kwana bakwai bayan ziyarar da ya gabata.

KU KARANTA: Zan iya kawar da 'yan Boko Haram ba tare da tallafin gwamnati ba, in ji Sunday Igboho

Sabon shugaban sojoji ya sake ziyartar jihar Borno a karo na biyu
Sabon shugaban sojoji ya sake ziyartar jihar Borno a karo na biyu Hoto: KOKO Tv Nigeria
Source: UGC

Dukkanin ziyarar biyu an ruwaito su ne domin cimma nasarar aiki a kokarin shawo kan matsalar ta'addanci a Arewa maso Gabas.

Shugaban ya sami cikakken bayani daga kwamandojin tsare-tsare daban-daban kan nasarorin da aka samu a kokarin da ake yi na kwantar da tarzomar.

Yayin da yake jawabi ga dakaru a sansanin soji na musamman da ke Ngamdu, ya yaba musu kan biyayyar da suka nuna a ci gaba da yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas.

Ya kuma bai wa sojojin tabbacin goyon baya da kuma kayan aiki masu kyau don bunkasa aikinsu.

A cikin ‘yan kwanakin nan, an ba da rahoton sansanonin masu tayar da kayar baya da yawa da sojoji suka kai hari kuma an kame wasu da ake zargi kuma an kashe wasu a hare-haren.

Sojojin sun yi zargin cewa sun gamu da cikas saboda yawaitar sanya nakiyoyi a wuraren da ba a san su ba daga masu tayar da kayar baya wadanda galibi kan lalata motoci, nakasa ko kashe mutane.

KU KARANTA: Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare

A wani labarin, Tukur Buratai, tsohon babban hafsan hafsoshin soja, ya ce ya yi rawar gani yayin da yake kan karagarsa a aikin soja, The Cable ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai a karshen mako a Abuja, Buratai ya ce akwai "kundi" na nasarorin da ya samu a Hedkwatar Tsaro dake magana kan kokari a aikinsa.

Ya yi magana ne a wani bikin dare da aka shirya wanda mambobin wata kungiya na Kwalejin Tsaro ta Najeriya ta shirya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel