Shirin ciyar da yara 'yan makaranta ya samar da ayyuka 14,000 a Neja, Jami'i

Shirin ciyar da yara 'yan makaranta ya samar da ayyuka 14,000 a Neja, Jami'i

- Wani jami'i a jihar Neja da ke kula da shirin ciyar da yara 'yan makaranta ya ce shirin ya samar da ayyukan yi

- Jami'in ya ce shirin ya samar da ayyukan yi ga sama da mutane 14,000 a fadin jihar Neja

- Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kara kudin abincin yaran duba da tabarbarewar tattalin arziki

Mista Umar Ndashacba, Manajan Shirye-shirye na Shirin Ciyar da Makarantun Gida na Kasa (NHGSFP) a Neja, ya ce aƙalla an samar da ayyuka sama da 14,000 a cikin shekaru biyu da kasancewar shirin a jihar.

Ndashacba ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

"Duk da cewa an kaddamar da shirin a jihar a shekarar 2018, ta samar da ayyuka sama da 14,000 ga mata da kuma baiwa manoma damar bunkasa noman."

Ya ce jihar tana da sama da dalibai 560,000 da suke cin gajiyar shirin wanda a cewarsa, da alama ya inganta karatunsu a makarantar firamare.

KU KARANTA: Zan iya kawar da 'yan Boko Haram ba tare da tallafin gwamnati ba, in ji Sunday Igboho

Shirin ciyar da yara 'yan makaranta ya samar da ayyuka 14,000 a Neja, in ji wani jami'i
Shirin ciyar da yara 'yan makaranta ya samar da ayyuka 14,000 a Neja, in ji wani jami'i Hoto: The Guardian
Source: UGC

“Shirin ya samar da ayyukan yi, ya bunkasa ayyukan noma tare da bai wa manoma kulawar da ake bukata.

“Manoman suna noman wake, shinkafa, waken soya, da sauransu kuma sune muke amfani da su a cikin tsarin abincin mu na yara.

“Shirye-shiryen sun samar da ayyuka sama da 14, 000 kuma karin ayyuka zasu zo yayin da muke ci gaba; muna da masu dafa abinci, da masu samar da kayayyaki na gida, da ofisoshi da kuma tawaga daban-daban,'' in ji Ndashaba.

Manajan NHGSFP na Neja, duk da haka, ya yi kira da a sake nazarin farashin abinci ga kowane yaro lura da yadda farashin kayan abinci ya sauya a kasuwa da kuma tattalin arziƙin da ke taɓarɓarewa sakamakon Cutar COVID-19.

“Duk da haka, muna fata cewa Gwamnatin Tarayya za ta kara farashin abincin kowane yaro,’" in ji shi.

KU KARANTA: Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare

A wani labarin, Wasu mata a jihar Kaduna sun koka kan zargin sama-da-fadi da son kai a cikin tallafin N20,000 da ke gudana wanda Ma’aikatar Kula da Jin Kai ta Tarayya ke yi a jihar, The Guardian ta ruwaito.

Matan sun yi magana da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Litinin a Kaduna a wurin da ake rabon kudin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel