PDP: Ba mu goyon bayan a ba Buratai, Siddique, Ibas, Usman da Olonisakin kujerar Jakadu

PDP: Ba mu goyon bayan a ba Buratai, Siddique, Ibas, Usman da Olonisakin kujerar Jakadu

- Jam’iyyar PDP ba ta goyon bayan a ba tsofaffin hafsoshi mukaman Jakadu

- PDP ta roki Sanatoci su ki yin na’am da wannan shiri da gwamnati ta ke yi

- Jam’iyyar adawar ta ce ana neman katange tsofaffin sojojin ne daga bincike

Jam’iyyar PDP ba ta yi na’am da zaben tsofaffin hafsoshin tsaro da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, da nufin ya ba su mukaman jakadu ba.

Babbar jam’iyyar hamayyar ta na zargin gwamnatin APC da Mai girma Muhammadu Buhari sun yi wannan ne domin a hana binciken tsofaffin hafsun.

PDP ta ce akwai kashin kisan gillar Bayin Allah da keta alfarmar Bil Adama da sojoji su ka yi a karkashin shugabancin tsofaffin hafsoshin tsaron kasar.

Jam’iyyar adawar ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ta bakin sakataren yada labaran ta na kasa, Kola Ologbondiyan, a ranar Alhamis da yamma.

KU KARANTA: IGP zai kara watanni 3 a ofis - Buhari

Kola Ologbondiyan ya yi wa jawabin na sa take da: “Zaben jakadun kasar waje: PDP ba ta goyon bayan a katange tsofaffin hafsoshin sojoji daga bincike.”

“PDP ta na kira ga Sanatoci su ajiye ra’ayin siyasa, su tsaya a bangaren jama’a, musamman wadanda barnar da tsofaffin hafsoshin su kayi ya fada kansu.”

Jam’iyyar ta ce raina hankalin ‘Yan Najeriya ne ace gwamnatin APC ta na neman yin amfani da kujerun Jakadu domin ta katange tsofaffin sojojin daga bincike.

“Yunkuri ne ido rufe na ba tsofaffin jagororin sojojin kariya daga bincike, da cafke su, da ma yiwuwar a gurfanar da su a gaban kotun Duniya na ICC.” Inji PDP.

KU KARANTA: Bayan kwanaki 8, Buhari ya dawo da Hafsun Sojoji cikin Gwamnati

PDP: Ba mu goyon bayan a ba Buratai, Siddique, Ibas, Usman da Olonisakin kujerar Jakadu
Buhari da Jami'an tsaro Hoto; Facebook
Asali: Facebook

“Daukar wannan mataki a lokacin da ICC ta tabbatar da shirinta na fara gudanar da bincike a kan zargin da ke wadannan mutane, ya tabbatar da rashin gaskiyarsu.”

PDP ta ce a maimakon tsofaffin sojojin su amsa laifin kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zanga a Lekki, da hallaka mutane a Zaria, sai ake nema ba su mukami.

A jiya ne ku ka ji cewa Muhammadu Buhari ya kara sunayen wadanda zai nada Jakadu, inda shugaban kasar ya aikawa 'yan majalisa sunayen tsofaffin hafsoshi.

Buhari ya nemi Sanatoci su ba shi damar nada Abayomi G. Olonisakin, Tukur Y. Buratai, Ibok-Ete Ibas, Sadique Abubakar da Mohammed S. Usman a matsayin Jakadu.

Jam'iyyar PDP mai adawa ta bukaci shugaban kasa Buhari ya janye wannan shiri da yake yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng