Allah kadai ya san gobe, Amaechi ya yi magana a kan wanda zai gaji Buhari

Allah kadai ya san gobe, Amaechi ya yi magana a kan wanda zai gaji Buhari

- An yi wa Ministan sufurin kasa, Rotimi Ameachi, tambaya kan siyasar 2023

- Rotimi Ameachi yace bai san wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba ba

- Jigon na APC ya ce aikin da ke gabansa shi ne sauke nauyin kujerar Minista

Ministan sufurin na kasa, Rotimi Chibukwe Amaechi, ya yi watsi da rade-radin da ake yi na cewa ana masa hangen zama shugaban Najeriya a 2023.

An yi hira da mai girma Ministan a gidan talabijin na Channels TV, inda ya bayyana cewa Ubangiji ne kadai ya san wanda zai zama shugaban Najeriya.

A cewar tsohon gwamnan kuma jagoran jam’iyyar APC a yau, aikin da ke gabansa shi ne sauke nauyin kujerar Minista ba harin takarar shugaban kasa ba.

KU KARANTA: Femi Fani Kayode na shirin komawa APC

“Har yanzu ni Ministan sufuri ne, kuma Ubangiji ne kawai zai iya cewa ga shugaban kasar Najeriya a 2023.”

Rotimi Amaechi ya yi gwamna sau biyu a jihar Ribas, kuma ya taba rike shugaban majalisar dokoki na Ribas, ya rike mukaman ne tsakanin 1999 da 2015.

Ko da yanzu akwai sauran lokaci mai tsawo kafin zaben 2023, mutane su na cigaba da tattauna yadda siyasar kasar za ta kasance a zaben mai zuwa.

A daidai lokacin da wa su ke ganin cewa ya kamata mulki ya koma yankin Kudancin kasar, akwai ‘yan siyasan Arewa da ake zargin su na harin takara.

KU KARANTA: 'Yan iskan gari sun kashe shugaban APC a Benuwai

Daga cikin wadanda ake zargin za su nemi kujerar shugaban kasa a 2023 akwai:

Atiku Abubakar

Bola Ahmed Tinubu

Rotimi Amaechi

Kayode Fayemi

Rabiu Musa Kwankwaso

Aminu Waziri Tambuwal

Donald Duke

Owelle Rochas Okorocha

Ahmed Sani Yarima

Yahaya Bello

David Umahi

Bala Mohammed

A baya kun ji cewa bangarorin jam'iyyar APC na jihar Zamfara sun amince da yin sulhu tare da aiki da juna tare domin tunkarar PDP a zaben 2023.

Bayan Mai Mala Buni ya samu yin sulhu a gidan jam'iyyar ta APC na Zamfara, an zabi tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari a matsayin shugaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel