Ministan Buhari ya bayyana inda aka kwana wajen aikin hako mai a yankin Arewa

Ministan Buhari ya bayyana inda aka kwana wajen aikin hako mai a yankin Arewa

- Ministan harkokin mai na Najeriya ya ce ana aikin hako mai a Jihohin Arewa

- Timipre Sylva ya bayyana kokarin da ake yi na samar da fetur a tafkin Chadi

- Mai girma Ministan ya ce annobar COVID-19 ta jawo cikas a ayyukan da ake yi

Karamin Ministan harkokin mai na Najeriya, Timipre Sylva, ya bayyana shirin da gwamnatin tarayya ta ke yi na hako mai a Arewa maso gabas.

Timipre Sylva ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi a shirin a gidan talabijin na Channels TV a wani shiri da ake kira Newsnight a jiya.

“Na fada a wasu lokuta cewa mun gano danyen mai a Arewa maso gabas, kuma mun fara aikin hake-haken shi a yankin tafkin Chadi.” Inji Sylva.

“Ban san ta yadda gano man zai yi tasiri a kan komai da komai ba, amma ta bangarenmu, mun yi imani cewa a ‘dan lokaci kadan, za a fara tatso man.”

KU KARANTA: An samu mai a Filato - NNPC

Ministan Buhari ya bayyana inda aka kwana wajen aikin hako mai a yankin Arewa
Ministan harkokin mai na Najeriya, Timipre Sylva
Asali: Twitter

Ministan ya koka da cewa annobar COVID-19 ya kawo ja-baya wajen harkar mai da gas a Duniya.

Mista Timipre Sylva ya yi magana game da taron da kasashen da ke karkashin kungiyar OPEC su ka yi ta kafar yanar gizo, ya ce a baya ba taba yin haka ba.

Minista tarayyar ya kuma yi magana game da satar danyen mai da fasa bututu da ake yi, ya ce an samu raguwar wadannan laifuffuka a wannan lokaci.

“Fasa bututun mai da ake yi ya ragu ba kamar da ba. A da ba mu samun 50% na abin da ya kamata a hako. Yanzu ina tabbatar maku abin ya ragu idan aka kamanta.”

KU KARANTA: Mun gano arzikin man fetur mai yawan gaske a Benuwai - NNPC

Mai girma Minista ya kuma yi bayani game da tashin kudin fetur da sakaci da aka yi a harkar gas, Sylva ya na ganin wannan laifi ne na gwamnatocin baya.

A farkon makon nan kun ji cewa farashin litar man fetur zai iya kai wa N200 kwanan nan a Najeriya saboda danyen mai ya yi kudi a kasuwannin Duniya.

Man fetur zai kara tsada idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari bai dawo da tallafi ba.'

Yan kasuwa suna ganin cewa ya kamata litar mai ta kai N200 a yau. Aalin yanzu ana saida fetur ne tsakanin N160-N165 a mafi yawan gidajen mai da ke kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng