Sheikh Gumi abokina ne, amma ba na tare da shi a kan yin wani sulhu da ‘Yan bindiga – El-Rufai

Sheikh Gumi abokina ne, amma ba na tare da shi a kan yin wani sulhu da ‘Yan bindiga – El-Rufai

- Nasir El-Rufai ya yi magana a game da matsalar garkuwa da satar mutane

- Gwamnan na Kaduna ya ce akwai bambamcin manufa tsakanin Gwamnoni

- El-Rufai ya soki yunkurin sulhun da wasu su ke yi da masu addabar jama’a

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da matsalar da jihohin Arewa maso yamma su ke fuskanta na miyagun ‘yan bindiga.

Mai girma Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya zanta da jaridar BBC Hausa, inda ya shaida cewa babu hadin-kai tsakanin jihohin yankin.

Malam Nasir El-Rufai ya ce akwai fahimta tsakaninsa da takwaransa na jihar Neja, amma a cewarsa, ba haka abin yake da sauran gwamnoni ba.

Nasir El-Rufai ya bayyana sabanin ra’ayi da bambancin fahimtar da ake samu da gwamnoni a matsayin abin da ya ke dawo da yakin da ake yi baya.

KU KARANTA: Abin da shugaban ƴan bindigan Zamfara ya faɗa mani - Gwamna

El-Rufai ya yi magana game da kokarin da Sheikh Ahmad Gumi yake yi, ya ce duk da cewa malamin abokinsa ne, amma ba ya tare da shi a nan.

“Laifin me aka yi masu, su da su ka kashe mutane, su ka kona gidajensu ne su ke neman diyya?”

A cewarsa, 'dan bindigan da ya saba karbar miliyoyin kudi ta hanyar garkuwa da mutane, ba zai koma saida dabbobi, ya na samun N100, 000 ko N200, 000 ba.

Gwamnan ya ce hadin-kan gwamnonin jihohi da taimakon gwamnatin tarayya wajen bada jami’an sojoji , shi ne zai kawo karshen wannan matsalar.

KU KARANTA: Babu sulhu da Miyagu - Sojojin Najeriya

El-Rufai: Sulhu da ake yi da Miyagun ‘Yan bindiga ya sa aka gaza samun zaman lafiya
Nasir El-Rufai da Ahmad Gumi Hoto: BBC Hausa
Asali: Facebook

Gwamnan jihar Kaduna ya na ganin a dage a kan yi wa masu satar dabbobi da garkuwa da mutane babu kakkautawa luguden wuta shi ne kurum mafita.

Gwamnatin jihar Zamfara ta na ganin cewa sulhu shi ne mafita, amma Nasir El-Rufai ya ce babu yadda za ayi wadannan hatsabiban ‘yan bindigan su tuba.

Kwanakin baya Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Zamfara, ya ce sun kammala tattauna wa da ‘dan shugaban ‘yan bindigan da aka kashe, Buharin Daji.

Gwamnan ya ce mutanen Jihar Zamfara sun ga amfanin yin sulhu da ‘yan bindiga. Matawalle ya ce wasu fitinannun tsagerun suna shirin mika wuya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel