Sabunta rijista a APC: Bata-gari sun aika da shugaban APC lahira a jihar Binuwai
- Rikici ya barke a taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar Benue ranar Lahadi, inda aka yi kare jini biri jini
- Sanadiyyar tashin hankalin har kashe shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Gboko ta Kudu akayi, Tersoo Ahu
- Kamar yadda bayanai suka gabata, wasu 'yan jagaliya ne suka kashe shi ana shirin fara rijistar 'yan jam'iyya a Gboko
Rikici da tashin hankali ya barke a wurin rijistar 'yan jam'iyyar APC a jihar Benue ranar Lahadi, hakan yayi sanadiyyar mutuwar shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Gboko, Tersoo Ahu.
Punch ta bayyana yadda wasu 'yan ta'adda suka rikita shiga wurin yin rijistar ana shirye-shiryen farawa a Gboko.
Ya kamata a fara rijistar ne a ranar Talata. Wani ganau ya bayyana yadda abin ya faru, inda yace, "Lokacin da aka fara horar da mutane a GRA, Gboko, mutane sun taru don su san wurin da za a fara rijistar da wadanda aka zaba da za su yi.
KU KARANTA: Kwamandojin ISWAP Sulum da Borzogo sun sha da kyar, soji sun kwace sansaninsu a Timbuktu
"Daga nan ne wurin ya rikice aka fara cece-kuce da musu iri-iri hakan ya janyo aka kashe shugaban."
Wani dan jam'iyyar wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce, "Da alamun rashin nasara ne ga jam'iyyar, wannan ya janyo aka dakatar da wasu 'yan jam'iyyar yayin da aka bar wasu su cigaba da rijistar.
"Wasu shugabannin jam'iyyar suna so su mayar da ita kamar wata kungiyar asiri kuma suna tunanin mutane za su bisu a haka."
Sakataren yada labaran jam'iyyar, James Orgunga, ya ce "Tabbas an kashe shugaban jam'iyyar na Gboko ta kudu. Ana tsaka da shirye-shiryen fara rijistar 'yan jam'iyyar wasu 'yan ta'adda suka kai masa farmaki, a nan take ya mutu."
KU KARANTA: 2023: Sahihan dalilan da suka sa Tinubu da Akande ke sukar sabunta rijista da APC ke yi
A wani labari na daban, a jiya ne majalisar dattawa ta bayyana cewa babu abinda zai sa a tirsasa ta tantance tare da tabbatar da nadin da shugaba Buhari yayi wa tsoffin hafsoshin tsaro.
A makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dattawa sunayen tsoffin hafsoshin tsaro a matsayin jakadu.
A yayin da kungiyar Yarabawa, Afenifere tace majalisar za ta iya tabbatar da tsoffin shugabannin tsaron amma bai dace shugaban kasan yayi wannan nadin ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng