An yi sulhu a jam'iyyar APC na Zamfara, an zabi Yari a matsayin shugaba

An yi sulhu a jam'iyyar APC na Zamfara, an zabi Yari a matsayin shugaba

- Daga karshe an samu fahimtar juna tsakanin bangarori biyu na jam'iyyar APC a jihar Zamfara

- Bangarorin biyu na tsohon Gwamna Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa sun amince za su yi aiki tare

- A yayin taron sulhun da aka yi ranar Lahadi a Kaduna, an zabi Abdulaziz Yari ya zama jagoran jam'iyyar a jihar

Bangarori biyu na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Zamfara sun amince da yin sulhu tare da aiki tare domin tunkarar zaben da ke tafe, The Punch ta ruwaito.

Dakta Mikailu Barau, jigo a jam'iyyar, ya sanar da sulhun cikin sanarwar bayan taro da ya fitar mai dauke da abubuwa 11 da suka amince a kai a taron da suka yi a ranar Lahadi a Kaduna.

An yi sulhu a jam'iyyar APC, na Zamfara, an zabi Yari a matsayin shugaba
An yi sulhu a jam'iyyar APC, na Zamfara, an zabi Yari a matsayin shugaba. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa bangarorin biyu, da tsohon gwamna Abdulazeez Yari ke jagoranta da tsagin Sanata Kabiru Marafa sun hallarci taron na sulhu.

Barau ya ce cikin abubuwan da aka amince a wurin taron shine zaben Yari a matsayin sabon shugaban jam'iyyar a jihar.

DUBA WANNAN: Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze

Tunda farko, bangarorin biyu, a ranar Lahadi, sun gana da kwamitin sulhu na rikon kwarya ta Gwamna Maimala Buni domin warware matsalolin da ke tsakaninsu a jihar.

"Magoya bayan Marafa da Yari duk sun amince da sulhun sannan sun yarda a yi aiki tare don gina jam'iyyar saboda ta karbe mulkin jihar Zamfara a nan gaba," a cewar wani sashi na sanarwar.

KU KARANTA: Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta, Gwamnatin Kogi

A cewar Barau, an soke dukkan shugabannin tsagin Sanata Marafa yanzu jam'iyyar ta zama daya karkashin jagorancin Yari.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164