Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare

Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare

- Wata mata ‘yar shekaru 50 ta nuna cewa shekaru ba komai bane face adadi kuma ba za ta iya tsayawa kan aikata kowane irin aiki ba

- Matar ta fara karatun sakandare a wata makaranta a jihar Kwara duk da shekarunta

- Ta kasance tana murmushi yayin da aka dauki hotonta tare da alkalami a hannu cikin kayan makarantar

Mashahurin magana mai cewa shekaru ba komai bane face lambobi sun taka rawa a rayuwar 'yar Najeriya. Wannan lokacin game da neman ilimi ne, Hausawa dai sun ce gemu baya hana ilimi.

Matar da ke da shekaru 50 an gan ta a makarantar sakandare yayin da take zaune don daukar karatun.

A wani rubutu da aka yi a Otujoleblog, matar da aka sakaya sunanta ta sanya kanta a matakin karamar makarantar sakandare, aji biyu a makarantar Ilorin Grammar School, Ilorin.

KU KARANTA: Zan iya kawar da 'yan Boko Haram ba tare da tallafin gwamnati ba, in ji Sunday Igboho

Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare
Gemu ba ya hana ilimi: Wata mata 'yar shekaru 50 ta shiga makarantar sakandare Hoto: @official_ojutoleblog
Asali: Instagram

A cikin hoton da aka watsa, ana iya ganin ta tana da nuna alamar wanda ke cikin farin ciki don cimma nasara a kan zama cikakkiyar 'yar makarantar sakandare sanye da ruwan hodan kaya da hular beret.

Bayan ta, mai yiwuwa tana kallon wanda ya ɗauki hoton, yara 'yan makaranta ne da ta girme su.

Hakanan ya bayyana cewa makarantar ta dukkan jinsi ce kamar yadda ake ganin yara maza suna zaune a bayanta, suma 'yan mata haka.

Babu wani bayani da aka bayar game da dalilin da ya sa ta yanke shawarar shigar da kanta a makaranta ko kuma shin ta yi karatun a baya amma abu daya ya bayyana - tana son yin karatu kuma ba za ta yarda shekarunta su hana ta ba.

KU KARANTA: Rashin aikin yi ne ya tilasta ni yin fashi, in ji wani matashi mai skekaru 23

A wani labarin, Fursunoni saba'in da shida na tsohuwar cibiyar kula da tsofaffin yara na Abeokuta, Ibara, jihar Ogun, sun kammala karatu daga kwalejin ilimi ta Yewa (YCCE).

Hukumar Kula da Yan Gidan Yari ta Kasa (NCoS) ce ta bayyana hakan, inda ta ce wasu 18 sun shiga karatu cikin kwasa-kwasai daban-daban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.