Nasarorin da na cimma sun kai a rubuta littatafai akai, in ji Burutai

Nasarorin da na cimma sun kai a rubuta littatafai akai, in ji Burutai

- Tsohon hafsin sojojin Najeriya ya bayyana cewa ba abu ne mai sauki ba irin nasarori da ya cimma

- Ya ce nasarorin da ya cimma sun kai a rubuta kundin littatafai domin yaba masa a aikinsa

- Ya kuma bayyana ritayarsa a matsayin mai mutunci da kuma cika alkawarin aiki

Tukur Buratai, tsohon babban hafsan hafsoshin soja, ya ce ya yi rawar gani yayin da yake kan karagarsa a aikin soja, The Cable ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai a karshen mako a Abuja, Buratai ya ce akwai "kundi" na nasarorin da ya samu a Hedkwatar Tsaro dake magana kan kokari a aikinsa.

Ya yi magana ne a wani bikin dare da aka shirya wanda mambobin wata kungiya na Kwalejin Tsaro ta Najeriya ta shirya.

Sai dai fadar shugaban kasar ta bayyana nadin nasu a matsayin tukuici saboda aiki tukuru.

"Ritaya ne mai mutunci da kuma alƙawari mai daraja. Ni ba dan siyasa ba ne, don haka ba ni da wata magana ga 'yan adawa. Na yi aiki mai kyau," in ji shi.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Hotunan bikin murnar yaye fursunoni 76 da suka kammala NCE na ta yawo a kafofin sada zumunta

Nasarorin da na cimma sun kai a rubutu littatafai akai, in ji Burutai
Nasarorin da na cimma sun kai a rubutu littatafai akai, in ji Burutai Hoto: This Day News
Source: UGC

“Na yi farin ciki cewa a cikin watan Yulin shekarar da ta gabata, jami’aina a hedikwatar sojoji sun tattara bayanan nasarori na. Ba zan iya tuna duk ayyukan da muka aiwatar ba.

“Shin ta fuskar kayan more rayuwa? Shin ta fuskar karfin iya aiki ne? Shin ta fuskar horo ne? Tunda aka nada ni, babu wani lokaci maras dadi dangane da horo.

"Ka tuna da darussa daban-daban - atisayen horo daga 'Python dance', 'Crocodile smile', har ma da na baya-bayan nan 'Exercise Sahel Sanity'.

"Ina tsammanin za ku iya rubuta kundin littattafai dangane da nasarorin da na samu dangane da irin bangaren da kuke son ɗauka."

Yayinda suke ofis, Buratai da tsoffin shugabannin hafsoshin sun sha suka saboda rashin kulawa da tayar da kayar baya a arewa maso gabas sosai.

KU KARANTA: Zan iya kawar da 'yan Boko Haram ba tare da tallafin gwamnati ba, in ji Sunday Igboho

A wani labarin, Wani matashi dan shekara 34 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, Sampson Ebiowei, ya bayyana cewa ya samu bindigarsa ta AK-47 ne daga hannun wani sojan Najeriya da ke aikin Operation Lafiya Dole a yankin Arewa maso Gabas.

Ya kuma kara da cewa sojan ya sayar masa da bindigar ne kan kudi N300,000, Sahara Reporters ta ruwaito.

Ebiowei, wanda ya fito daga Ofunama a karamar hukumar Ovia South West West na jihar Edo, ‘yan sanda sun cafke shi da bindiga da kuma alburusai 88.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel