Zan iya kawar da 'yan Boko Haram ba tare da tallafin gwamnati ba, in ji Sunday Igboho
- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya kirayi a bai wa Sunday Igboho dama wajen yakar Boko Haram
- Sunday Igboho, a baya cikin shekarar 2020 ya yi ikrarin gama wa da 'yan Boko Haram ba tare da taimakon gwamnati ba
- Duba da ayyukansa na baya-bayan nan, Shehu sani ya rubuta a shafin Twitter da a baiwa Sunday dama
Shahararren mai rajin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya bayyana cewa yana da cikakken shiri da ya kamata don yaki da Boko Haram ba tare da goyon bayan gwamnati ba.
Igboho ya yi wannan bayanin ne a wata hira ta bidiyo da aka fitar a shekarar 2020.
Ya ce: "Abin da zan yi amfani da shi wajen yaki da Boko Haram, ina da shi tuni."
Bidiyon ya sake bayyana bayan da tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gayyaci Igboho don taimakawa wajen fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram daga dajin Sambisa.
KU KARANTA: Rashin aikin yi ne ya tilasta ni yin fashi, in ji wani matashi mai skekaru 23
Bayan ayyukan Igboho na baya-bayan nan, wadanda ya ce na kawar da makiyaya a yankin Kudu maso Yamma, Sani ya ce Igboho na iya taimakawa wajen kawo karshen ta’addanci a kasar nan, musamman a Arewa maso Gabas, idan aka ba shi dama.
Da yake magana a shafinsa na Twitter, Sani ya ce: "A gayyaci Sunday don taimakawa wajen fatattakar BH (Boko Haram) daga Sambisa."
Ana daukar babban dajin Sambisa a matsayin daya daga cikin wuraren da kungiyar Boko Haram dake ikirarin jihadi ke amfani da shi a matsayin matattarar su tare da yin garkuwa da mutane.
Sunday ya bayyana shirinsa na ikon yakar Boko Haram ba tare da wani gwamna ya tallafa masa ba.
Sunday Igboho yana cewa; “Matasan Yarbawa ne kawai idan za mu iya yarda mu yi fada. Ba na neman komai daga kowa, abin da zan yi amfani da shi wajen yaki da Boko Haram, ina da shi.
“Bana bukatar komai daga wani gwamna saboda wani gwamna zai yi kokarin neman kudi daga gare ta. Zai yi iƙirarin cewa ya kashe wani adadi akan Amotekun kuma ya sami riba daga gare ta. Wannan ba zai haifar da wani abu mai kyau ba.
Igboho ya kuma ce lokaci zai zo da mutane za su tashi don kare filayen su.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta dawo da 'yan gudun hijirar Borno 4,982 daga Kamaru
A wani labarin, Jami’an ‘yan sanda da ke aiki a Operation Puff Adder karkashin jagorancin DPO Kaura Namoda a jihar Zamfara sun taimaka wajen sakin wasu mutane biyar ba tare da biyan fansa ba, Daily Trust ta ruwaito.
Mutane biyar da suka ceto din sune wadanda aka sace a kusa da makarantar Sakandiren Namoda da Zangon Danbade na karamar hukumar Kaura Namoda.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng