Wani soja ya sayarwa dan fashi da bindigarsa kirar AK-47 kan kudi N300,000

Wani soja ya sayarwa dan fashi da bindigarsa kirar AK-47 kan kudi N300,000

- Rundunar 'yan sanda sun kame wani dan fashi da makami a jihar Edo, ya kuma bayyana inda ya samu bindiga

- Ya bayyana cewa wani soja ne dake aiki a jihar Borno ya sayar masa da bindigar N300,000

- Dan fashin ya kuma bayyana cewa hanashi wani albashi ne ya tunzura shi fara yin fashi

Wani matashi dan shekara 34 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, Sampson Ebiowei, ya bayyana cewa ya samu bindigarsa ta AK-47 ne daga hannun wani sojan Najeriya da ke aikin Operation Lafiya Dole a yankin Arewa maso Gabas.

Ya kuma kara da cewa sojan ya sayar masa da bindigar ne kan kudi N300,000, Sahara Reporters ta ruwaito.

Ebiowei, wanda ya fito daga Ofunama a karamar hukumar Ovia South West West na jihar Edo, ‘yan sanda sun cafke shi da bindiga da kuma alburusai 88.

Ebiowei ya bayyanawa 'yan sanda cewa ya samu bindigar ne kuma ya fara harkar satar mutane bayan da aka cire sunansa daga jerin wadanda ke cin gajiyar Shirin Afuwa na gwamnatin Niger-Delta na 'yan ta’addan da suka tuba.

KU KARANTA: Jihar Sokoto ta kashe N740m akan rajistar WAEC da NECO na dalibai a jihar, in ji Tambuwal

Wani soja ya sayar da bindigarsa kirar AK-47 kan kudi N300,000
Wani soja ya sayar da bindigarsa kirar AK-47 kan kudi N300,000 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ebiowei, wanda ke da mata uku da yara hudu, ya ce, “An sanya ni ne a cikin shirin afuwa na Gwamnatin Tarayya a da, kuma ana biyana N65,000 a kowane wata, amma kawuna da ya taimake ni na samu aikin ya ce yana son zai ke karbar N20,000 daga cikin kudin.

“Sai dai, saboda na ce a’a, ya cire sunana daga shirin.

“Cikin fushi, na tuntubi wani soja da abokina da ke aiki a Maiduguri wanda ya sayar mini da bindigar a kan N300,000 tare da harsasai 88. Na sayi bindigar ne don yaki da kamfanonin mai a wurinmu, saboda sun ki ba mu aiki.”

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Philip Ogbadu, wanda ya gabatar da Ebiowei tare da sauran wadanda ake zargi 11 da sace mutane.

A cewar Ogbadu, rundunar za ta hada kai da mafarautan yankin, ‘yan banga, da kuma hukumomin 'yan uwa don kawo karshen aikata laifuka a jihar.

KU KARANTA: Rashin aikin yi ne ya tilasta ni yin fashi, in ji wani matashi mai skekaru 23

A wani labarin, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta gano wani kauyen da ake nomar wiwi a karamar hukumar Owan West ta jihar Edo, The Cable ta ruwaito.

Buba Wakawa, kwamandan NDLEA a Edo, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Benin, babban birnin jihar.

Ya ce rundunar ta cafke wasu mutane bakwai wadanda ke boye wiwi a manyan rumbunan adana kaya guda hudu a dajin Ukpuje da ke Owan West.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel