Rashin aikin yi ne ya tilasta ni yin fashi, in ji wani matashi mai skekaru 23
- Rundunar 'yan sandan jihar Legas sun samu nasarar cafke wasu bata-gari a wani samame
- Sun kame wasu matasa da zargin aikata mummunan laifin fashi da makami a cikin al'umma
- Daya daga cikinsu, ya bayyana cewa rashin aikin yi ne ya tilasta shi aikata fashi da makami
Wani matashi dan shekaru 23 da ake zargi da fashi da makami, Michael Ogungbade, wanda aka kama saboda ya afkawa mutane a yayin zirga-zirga ya yi ikirarin shiga aikata laifin sakamakon rashin aikin yi, Daily Trust ta ruwaito.
Ogungbade na daga cikin mutane 27 da ake zargi da aikata laifi da jami’an ‘yan sanda suka kama a Legas wadanda suka kai farmaki maboyarsu a cikin tsakiyar birnin Legas.
Samamen ya biyo bayan korafe-korafen hare-hare kan mutanen da ke kan ababen hawa yayin da suke cikin zirga-zirga.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta dawo da 'yan gudun hijirar Borno 4,982 daga Kamaru
Ya fada wa manema labarai a hedikwatar rundunar, Ikeja, cewa duk kokarin da ya yi a baya don ganin ya samu aiki bai yi nasara ba.
Ya ce, "Domin neman tsira daga yunwa, na shiga sahun wasu samari a Abule-Egba don karbar kudi daga 'yan kasuwa."
Kakakin ‘yan sanda na Legas, Muyiwa Adejobi, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce an kuma kama wasu mutane 27 da ake zargi biyo bayan korafin hare-haren wadanda abin ya shafa.
Adejobi ya ce, “Jami’an rundunar Rapid Response Squad (RRS) ne suka yi nasarar cafke wadanda ake zargin biyo bayan umarnin kwamishinan 'yan sanda (CP) ga kwamandan RRS, CSP Olayinka Egbeyemi."
"Wadanda aka kama sun hada da Olajide Kolawole mai shekaru 26, Kehinde Ayoola mai shekaru 25, Dola Abdullahi mai shekaru 20 da Michael Ogungbade mai shekaru 19."
KU KARANTA: Ya kamata 'yan Najeriya su daina tsoma gwamnati a harkar kudin Hajji, in ji NAHCON
A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a Adamawa, a ranar Lahadi, ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da zama mamba a wata kungiyar gungun masu laifi da aka fi sani da‘ Shila Boys' a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa.
Wasu ‘yan zanga-zanga sun kona dan kungiyar Shila har lahira bisa zargin cewa ya yi wa wata mata sata da kuma daba mata wuka, Daily Trust ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng