Scholarship: Likitoci mata 47 'yan jihar Kano sun dawo bayan kammala karatu a Sudan

Scholarship: Likitoci mata 47 'yan jihar Kano sun dawo bayan kammala karatu a Sudan

- Wasu mata da gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin karatunsu zuwa kasar Sudan sun dawo ranar Juma'a

- Rahotanni sun bayyana cewa mata liktoci sama 40 ne suka sauka a filin jirgin Aminu Kano dake Kano

- Gwamnatin jihar ta karbesu hannu bibbiyu tare da kaddamar liyafar murnar dawowansu

Akalla likitocin mata 47 'yan jihar Kano sun dawo daga Sudan bayan sun kammala karatunsu cikin nasara wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyi, Premium Times ta ruwaito.

Abba Anwar, babban sakataren labarai na gwamnan, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Kano.

Sabbin daliban da suka kammala karatun aikin likita sun tafi kasar Sudan tun a shekara ta 2014 amma sun gamu da kalubale kan biyan kudade kafin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta warware dukkan matsalolin.

Wannan ya share fagen kammala karatun su na MBBS a Jami'o'in Al-Ahfad, Al-Razi da Umdurman a Sudan.

KU KARANTA: Buhari zai kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ranar Talata

Scholarship: Likitoci mata 47 'yan jihar Kano sun dawo bayan kammala karatu a Sudan
Scholarship: Likitoci mata 47 'yan jihar Kano sun dawo bayan kammala karatu a Sudan Hoto: The Vanguard News
Asali: UGC

A cewar sanarwar, likitocin sun isa filin jirgin sama na Aminu Kano (MAKIA) a daren Juma'a.

Sun samu rakiyar Muhuyi Rimingado, Shugaban zartarwa na korafin jama'a da Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Da yake jawabi a wajen liyafar karramawar da aka yi wa likitocin a Kano, Mista Rimingado ya ce gwamnati ta kuduri aniyar bankado duk wasu munanan ayyuka da ake zargin suna da alaka da shirye-shiryen ba da tallafin karatu na kasashen waje.

“Wannan shine dalilin da yasa gwamnan ya umarci ofishin mu da ya shigo cikin aikin.

“Iyaye su sani cewa, daga fiye da dala miliyan 2 da aka nufa don wannan aikin, gwamnatin Gwamna Ganduje ta biya sama da rabin kuɗin.

"Wato, an biya sama da dala miliyan 1," in ji shi.

KU KARANTA: Baya ga Najeriya, akwai kasashe bakwai da suka haramta cinikin Bitcoin

A wani takaitaccen jawabi, Kwamishiniyar Ilimin Sama da Sakandare, Mariya Bunkure, ta yaba da kokarin da gwamnati ta yi na taimaka wa likitocin su kammala karatunsu cikin nasara.

“Wannan gwamnatin a shirye take ko yaushe don ci gaban dan Adam.

“Gwamna Ganduje ya yi imani da bunkasa matasan mu; yana so ya tabbatar da cewa mata sun yi karatu daidai, a matsayin wani bangare na masu ruwa da tsaki don ci gaban jiharmu baki daya,'' in ji Mista Bunkure.

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gargadi malaman addinin Islama da su daina yin kalamai masu tayar da hankali, wadanda za su iya keta zaman lafiya, yayin wa’azi, The Guardian ta ruwaito.

Ganduje ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Kano lokacin da ya gana da Limamai na Masallacin Juma’at da sauran malaman addinin Musulunci a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel