'Yan Nijeriya 802 da suka makale a Saudiyya za su dawo yau
- Wasu 'yan Najeriya da aka kame a kasar Saudiyya da laifin haure ba kan ka'ida ba zasu dawo Najeriya yau
- A yau Alhamis, ana sa ran dawowar kimanin 'yan Najeriya sama da 800 a Abuja
- Ana kuma sa ran dawowar sauransu a jirgi na biyu a ranar Juma'a
Ana sa ran wasu 'yan Najeriya 802 da suka makale a masarautar Saudiyya za su sauka a Abuja yau da gobe, Daily Trust ta ruwaito.
An tsare su a wurare daban-daban da ake tsare mutane a Saudiyya kan batun kaura ba bisa ka'ida ba.
Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Harkokin Waje, Gabriel Aduda, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce za a karbi wadanda za su dawo din ne a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta hanyar jiragen sama biyu na Saudiyya.
KU KARANTA: NIMC ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin NIN
“Za a kebe su a sansanin alhazai na FCT na tsawon kwanaki 14 daidai da ka’idojin da aka kafa na COVID-19.
“Rukunin farko zai zo ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Janairu da karfe 11:50 na safe, yayin da na biyu zai zo ranar Juma’a, 29 ga watan Janairu da karfe 10:35 na safe.
“Wadanda za su dawo din za a karbi bakuncin dawowarsu ne daga jami’an ma’aikatar harkokin waje, da kwamitin shugaban kasa kan COVID-19 da sauran MDA da suka dace.
"Bayan haka, ma'aikatar za ta sauƙaƙe hanyoyin zuwa garuruwansu na asali".
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara rabawa mata N20,000 a jihar Kaduna
A wani labarin, Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), a ranar Litinin, ta fada wa shugabannin hukumomin mahajjata na jihohi su ci gaba da rajista da shirye-shiryen aikin Hajji da Umrah na 2021.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban ta na Hulda da Jama'a, Fatima Sanda, Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunke Hassan, ya ce dage dakatarwar jiragen saman kasashen duniya da Masarautar Saudi Arabiya ta yi, ya ba da babban fatan yiwuwar maniyyatan su tashi domin aikin Hajji da Umrah a bana.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng