‘Yan sanda sun ceto wadanda aka sace su 5, sun kwato shanu 11 a Zamfara

‘Yan sanda sun ceto wadanda aka sace su 5, sun kwato shanu 11 a Zamfara

- 'Yan sanda a jihar Zamfara sun samu nasarar ceto wasu mutane biyar da aka sace

- Hakazalika sun kwato shanu 11 da ake zargin su ma na sata ne a hannun 'yan fashin

- 'Yan sandan sun sada wadanda aka ceton ga iyalansu bayan kaisu asibiti don binciken lafiya

Jami’an ‘yan sanda da ke aiki a Operation Puff Adder karkashin jagorancin DPO Kaura Namoda a jihar Zamfara sun taimaka wajen sakin wasu mutane biyar ba tare da biyan fansa ba, Daily Trust ta ruwaito.

Mutane biyar da suka ceto din sune wadanda aka sace a kusa da makarantar Sakandiren Namoda da Zangon Danbade na karamar hukumar Kaura Namoda.

KU KARANTA: Jama'ar gari sun cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola

‘Yan sanda sun ceto wadanda aka sace su 5, sun kwato shanu 11 a Zamfara
‘Yan sanda sun ceto wadanda aka sace su 5, sun kwato shanu 11 a Zamfara Hoto: Nigeria Police Force
Asali: UGC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya fada a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, cewa duk wadanda aka kubutar sun sami kulawa daga likitoci kuma 'yan sanda sun yi musu bayani sannan daga baya suka hada su da danginsu.

Ya ce, wata tawagar jami'an 'yan sanda ta gano shanu 11 da ake zaton na sata ne a karamar hukumar Maradun.

KU KARANTA: NDLEA ta bankado wani kauyen wiwi, ta cafke kwayoyi ‘masu darajar N1.4bn’ a Edo

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu masu satar mota su biyu a yankin Nassarawa na babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da aka fi sani da Western bypass, Daily Trust ta ruwaito.

‘Yan sanda sun kuma gano karamar mota kirar Toyota Camry dauke da lambar rajista ABC 590 DX da Toyota Corolla mai launin toka dauke da lambar rajista KTN 304 AG, daga wadanda ake zargin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel