'Yan sandan Kaduna sun kame masu satar motoci, an kwato wasu motoci

'Yan sandan Kaduna sun kame masu satar motoci, an kwato wasu motoci

- Wata rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna sun samu nasarar cafke wasu bata-gari a jihar

- Sun kame mutanen biyu ne dumu-dumu da zargin laifin satar motoci a cikin jihar Kaduna

- Sun kuma samu nasarar kwato motoci daga hannun barayin, yayin da suka bayyana lambobin motocin

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu masu satar mota su biyu a yankin Nassarawa na babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da aka fi sani da Western bypass, Daily Trust ta ruwaito.

‘Yan sanda sun kuma gano karamar mota kirar Toyota Camry dauke da lambar rajista ABC 590 DX da Toyota Corolla mai launin toka dauke da lambar rajista KTN 304 AG, daga wadanda ake zargin.

KU KARANTA: Ci gaba: Wasu mutane 18 sun kammala digiri a gidajen kaso a Najeriya

'Yan sandan Kaduna sun kame masu satar motoci, an kwato wasu motoci
'Yan sandan Kaduna sun kame masu satar motoci, an kwato wasu motoci Hoto: This Day
Asali: UGC

A cewar kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 2 ga watan Fabrairun 2021, daga jami’an rundunar da ke aiki a sashen Kakuri yayin da suke sintiri a kan babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da ke kan hanyar Nassarawa Bridge a Kaduna.

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Abubakar Abdullahi na Hayin Danmani da Gambo Musa na yankin Rigasa, duk a karamar hukumar Igabi ta jihar.

KU KARANTA: Kiran dukkan makiyaya da sunan ‘makasa’ na iya haddasa yaki a kasar nan, in ji El-Rufai

A wani labarin, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta cafke wani dan kasuwa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe (NAIA), Abuja da wani mutum a filin jirgin saman Murtala Mohammed (MMIA), Lagos, ‘tare da hodar iblis mai nauyin kilogram uku.’

Mai magana da yawun hukumar, Mista Jonah Achema, ya fada a ranar Alhamis a Abuja cewa yayin da “aka kama Adeleke Kazeem Biola a filin jirgin saman Legas tare da kilogram 1.5 na hodar Iblis a ranar Laraba, 3 ga Fabrairu 2021 a yayin tantance fasinjoji a jirgin Emirate zuwa Dubai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel