Chris Ngige yayi karin bayani a kan ragin N5 a kudin man fetur a makon gobe

Chris Ngige yayi karin bayani a kan ragin N5 a kudin man fetur a makon gobe

- Ministan kwadago ya sanar da rage farashin man fetur a Najeriya

- Chris Ngige ya ce za a samu kusan ragin N5 a kudin litar man fetur

- Za a samu sauki ne saboda NNPC zai dauki wasu dawainiyar man

A yau Talata, 8 ga Watan Disamba, 2020, mu ke jin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince ta rage farashin litar PMS watau man fetur.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto cewa Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa, Chris Ngige ya bayyana cewa za su rage farashi.

Sanata Chris Ngige ya yi wa ‘yan jarida wannan jawabi ne bayan ya yi wata gana wa da shugabannin kungiyoyin kwadagon Najeriya.

Da yake magana dazu a birnin tarayya Abuja, Chris Ngige ya ce an ci ma matsayar rage kudin man ne a sakamakon karin da aka yi kwanan baya.

KU KARANTA: An kara kudin mai zuwa kusan N170

Litar fetur ya kara kudi daga N160 zuwa N170, Ngige yace daga ranar Litinin mai zuwa, za a shigo da sabon farashin da za a rika saida litar man.

Kamar yadda rahotannin suka bayyana, ana sa ran zuwa ranar 14 ga watan Disamba, man ya rage kudi.

Daga cikin abin da gwamnatin tarayya tayi la’akari da shi wajen rage farashin man shi ne kara kudin shan wutar lantarki da aka yi kwanaki.

“Tattaunawar mu da NNPC ta yi kyau domin kamfanin ne ke shigo da mafi yawan mai cikin kasa.”

KU KARANTA: Direbobi, Masu Keke-Napep da Acaba za su mori tsarin MSME

Chris Ngige yayi karin bayani a kan ragin N5 a kudin man fetur a makon gobe
Dr. Chris Ngige Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

“Ragin zai sa a samu saukin kusan N5 a lita, kuma tsarin sabon farashin zai fara aiki ne a ranar Litinin, mako guda daga yau.” Inji Dr. Ngige.

Ngige yace mai bai karye a Duniya ba, dawainiyar da NNPC za tayi ya sa aka rage farashin.

A watan Nuwamba ne ku ka ji cewa an gano arzikin man fetur mai dimbin yawa kwance a jihar Benue da ke yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya.

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya watau NNPC, Mele Kolo Kyari ya bayyana wannan. Kyari ya yi wannan jawabi ne a taron kungiyar NAPE.

Idan za ku tuna NNPC da masana ilimin ma'adinan Najeriya ke jagorantan hakon mai da ake yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel