Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya za ta zauna a kan rahoton farashin wuta, fetur

Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya za ta zauna a kan rahoton farashin wuta, fetur

- Wakilan Gwamnatin Tarayya za sa su sake zama da bangaren ‘Yan kwadago

- Chris Ngige yace za su tattauna rahoton farashin fetur da kudin shan lantarki

- A 2020 ne Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kara kudin litar mai da na wuta

Gwamnatin tarayya za ta koma tebur da kungiyoyin kwadago a ranar 22 ga watan Fubrairu, 2021 kan maganar farashin litar man fetur da kudin lantarki.

Jaridar Punch ta rahoto Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa, Chris Ngige, ya na wannan bayani lokacin da ya zanta da ‘yan jarida ranar Litinin.

Sanata Chris Ngige ya ce zai yi taro da ‘yan kwadagon ne domin ayi la’akari da rahoton da kwamitocin da aka kafa ya yi a kan batun kudin mai da lantarki.

Hakan na zuwa ne bayan Chris Ngige da wakilan gwamnatin tarayya sun yi zama da kungiyoyin kwadagon a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Lai Mohammed da Garba Shehu ne su ke batawa Buhari suna – CNPP

Ngige ya ce sun karbi aikin da kwamitin da kwararrun da aka nada su kayi a kan batun farashin man fetur, sannan ana sauraron rahoton kwamitin kudin wuta.

Ministan ya fada wa ‘yan jarida cewa kungiyoyin kwadago sun bukaci a kara masu lokaci domin su yi wa rahoton farashin litar man fetur kallo da idanun basira.

“Aiki ne na kwararru, don haka su ka nemi kwararrun su sake yin bincike game da rahoton. Kwamitin da ke aiki a kan kudin shan wuta bai gama aiki ba.”

“Mu na tsammanin su kawo rahotonsu nan da mako guda, saboda haka za mu zauna a ranar 22 ga watan nan domin mu karbi duka rahoton.” Inji Sanata Ngige.

Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya za ta zauna a kan rahoton farashin wuta, fetur
Sanata Chris Ngige Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Babu mamaki a bada umarni a sake rufe makarantu - PTF

Tsohon ma’aikacin NNPC, Onochie Anyaoku ya jagoranci aikin duba litar fetur. Ana wannan zama ne da ‘ya ‘yan kungiyar NLC, TUC, PENGASSAN da kuma NUPENG.

Kwanaki an samu sauyin farashin shan wuta, amma karamin Ministan kwadago, Festus Keyamo ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta yi karin kudin wutar lantarki ba.

Da yake jawabi a Abuja, Keyamo ya bayyana cewa an yi wa wasu ‘yan kwaskwarima ne kurum a kan farashin shan wutan, amma abin bai kai ga karin farashi ba.

Ministan ya kira taro, yace hukumomi da kamfanoni ba su tuntube su kafin su dauki matakin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel