Buhari ya amince da bai wa sabbin jami’o’i 20 masu zaman kansu lasisi
- Gwamnatin tarayya ta amince da bude sabbin jami'o'i masu zaman kansu a taron FEC na yau
- An bayyana sunayen jami'o'in da gwamnatin ta yarda a basu lasisin wucin gadi a kasar
- An lissafo sunayen jami'o'i ashirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu
Majalisar zartarwa ta tarayya, FEC, a ranar Laraba, ta amince da kafa karin jami’o’i 20 masu zaman kansu a kasar.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa amincewar ta biyo bayan wani rubutu da Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya gabatar yayin taron yau wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Tara daga cikin jami’o’i masu zaman kansu suna Arewa maso Tsakiya, uku a Kudu maso Kudu, biyu a Kudu maso Gabas, biyar daga cikinsu a Arewa maso Yamma da kuma daya a Kudu maso Yamma.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron, Ministan ya ce jami’o’in da aka amince da su za su samu lasisinsu na wucin gadi daga Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, NUC.
KU KARANTA: Akwai shirin barkewar rikici na kabilanci da addini a wasu jihohi, DSS
Ya ba da sunayen cibiyoyin da aka amince da su kamar haka Jami'ar Topfaith, Mkpatak a Jihar Akwa Ibom; Thomas Adewumi University, Oko-Irese a Jihar Kwara; Jami'ar Maranathan, Mgbidi a Jihar Imo da Jami'ar Ave Maria, Piyanko a Jihar Nasarawa.
Sauran sune Jami'ar Mudiame, Irrua a jihar Edo; Jami'ar Havilla, Nde-Ikom a Jihar Kuros Riba; Jami'ar Claretian ta Nijeriya, Nekede a Jihar Imo; Jami'ar NOK, Kachia a Jihar Kaduna, Jami'ar Karl-Kumm, Vom a Jihar Filato da Jami'ar Al-Istiqama, Sumaila a Jihar Kano.
Har ila yau, an amince da Jami'ar James Hope, Legas a Jihar Legas; Maryam Abacha American University of Nigeri Kano a Jihar Kano; Jami'ar Babban Birni, Kano a Jihar Kano; Jami'ar Ahman Pategi, Pategi a Jihar Kwara, da Jami'ar Offa, Offa a Jihar Kwara.
Sauran sune Jami'ar Mewar, Masaka a Jihar Nasarawa, Jami'ar Edusoko, Bida a Jihar Neja; Jami'ar Philomath, Kuje a Abuja; Jami'ar Khadija, Majia a Jihar Jigawa da Jami'ar Anan, Kwall a Jihar Filato.
KU KARANTA: Adadin masu fama da talauci a Najeriya zai karu zuwa sama da 15m
A wani labarin, Akwai alamu masu karfi a daren Talata cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Sufeto-Janar na ’Yan sanda Mohammed Adamu ya mika mukaminsa. Adamu ya kammala aikinsa na shekaru 35 a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.
An sa ran zai mika shi ga babban jami'in da ke bakin aiki a ranar Litinin, amma bai yi hakan ba, yana kara jin cewa za a iya kara masa aiki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng