Bashir Bolarinwa ya bada labarin rigimar da kaure wajen rajistan APC a Jihar Kwara

Bashir Bolarinwa ya bada labarin rigimar da kaure wajen rajistan APC a Jihar Kwara

Yadda aka yi wa Shugaban rikon kwaryan APC da mutanensa ‘dan karen duka a taro- Hon. Bashir Bolarinwa ya fadi yadda wajen taron jam’iyyar APC ya koma filin daba

- Shugaban APC na jihar Kwara ya zargi mutanen Gwamna da dauko hayar tsageru

- An lakadawa Jagororin jam’iyyar APC duka, sannan an jawo sun yi asarar dukiya

Vanguard ta ce Bashir Bolarinwa, shugaban riko na jam’iyyar APC a Kwara ya bada labarin yadda aka auka masu da hari a wajen zaman jam’iyya da aka kira a Ilorin.

Bashir Bolarinwa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan an kira su zuwa wajen rajistar da kwamitin Sanata John Danboyi ya ke yi a dakin taro na Banquet Hall.

A cewar Bolarinwa, har zuwa karfe 1:30 na rana, ba a bude wurin da aka ce za ayi taro da karfe 12:00 ba. Wannan ya sa a aikawa Sanata Danboyi sako ta wayar salula.

“Ban san cewa wasu mutanen Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq su na cikin dakin taron ba. A inda mu ke a waje, an dauko hayar tsageru, amma ba mu dabu ba.”

KU KARANTA: Lai, Gbemi Saraki sun huro wa Gwamna AbdulRazaq wuta a APC

Ya ce: “Zuwa karfe 2:000 sai aka bude dakin taron, a lokacin da mu ke kokarin shiga ciki, sai wata cikin magoya bayan AA ta taso ta rike mani riga, ta hana ni shiga dakin.”

Hon. Bolarinwa ya ce na-kusa da shi sun taka wa wannan mata burki. Daga nan ya shiga dakin taron, ya na kutsa kai, sai ya ga dinbin mutanen gwamna sun cika wurin.

“Babu wanda aka bari ya shiga sai mutanen AA. Shugaban kwamitin rajistar, Danboyi, ya ga abin da ya faru, sai ya ce shi ne ya gayyato ni da sauran masu ruwa da tsaki.”

“Abin ya rincabe ya fi karfin kowa domin an dauko hayar ‘yan iska. Wasu cikin yaran nan sun zo da bindigogi, su ka fara kai wa mutanenmu hari, su ka rusa mana motoci.”

Bashir Bolarinwa ya bada labarin rigimar da kaure wajen rajistan APC a Jihar Kwara
Bashir Bolarinwa Hoto: www.today.ng
Source: UGC

KU KARANTA: An tashi baram-baram a taron APC a Kwara

“An yi raga-raga da motar shugabar mata ta jam’iyya, an lalata motar jigon jam’iyya, Wahab Adesina, kuma an ji masa rauni.” A karshe dai ba a iya yin zaman ba.

Shugaban rikon kwaryar na APC ya kara da: “Yanzu haka da na ke magana, an yi wa ma’ajin jam’iyya duka har ya shiga gargara, sun kuma karbe mabudin motarsa.”

Rahotanni sun zo mana kwanan nan cewa sabuwar Jam’iyyar su Ghali Umar Na-Abba, Kingsley Moghalu, da Hakemm Baba-Ahmed za ta shigo gari kafin zaben 2023.

‘Yan siyasar nan sun yi taron-dangi ne sun shirya kafa wata babbar Jam’iyyar siyasa ta hadaka.

Jagororin wadannan tafiya su ne: Olisa Agbakoba, Pat Utomi, Remi Sonaiya, Obadiah Mailafia, Issa Aremu, Chidi Odinkalu, Precious Elekima, da kuma Ezekiel Nya-Etok.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel