Sam Ohuabunwa ya bayyana niyyar sa ta neman takarar Shugaban kasa a 2023
- Sam Ohuabunwa ya ce da shi za ayi takarar Shugaban kasa a zaben 2023
- Ohuabunwa ya bayyana haka da aka yi hira da shi a gidan TV360 Nigeria
- Masanin ya ce ya gaji da tsayawa a gefe ya na ba ‘Yan siyasa shawarwari
Tsohon shugaban kungiyar Nigeria Economic Summit Group Sam Ohuabunwa ya fito ya bayyana aniyarsa na neman takarar kujerar shugaban kasa a 2023.
Fitaccen masanin ya yi hira da gidan talabijin na TV 360 Nigeria a makon da ya gabata, inda ya bayyana cewa zai so a ce ya zama magajin Muhammadu Buhari.
Premium Times ta ce Ohuabunwa shi ne shugaban kungiyar Pharmaceutical Society of Nigeria.
“A shekaru na da lokaci na, ba zan fito da wasa ba. Ba shahara na ke nema ba … takara na ke yi da gaske.” Ohuabunwa mai shekara 70 ya fada wa TV360 Nigeria.
KU KARANTA: An kashe N1b wajen yi wa ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC rajista a 2014 - Akande
Ohuabunwa ya ce ya ‘tsere wa’ siyasa na tsawon lokaci a Najeriya, amma har yanzu abubuwa sun ki yin kyau, don haka ya ga lokaci ya yi da zai fito gadan-gadan.
Masanin ya bayyana shigowarsa takara da abin da ya faru da Yunusa a Injila wanda ya yi wa al’umma wa’azi bayan ya shafe tsawon kwanki a cikin tumbin kifi.
“Mun yi siyasar kudi na tsawon lokaci, ina tunanin mutanen Najeriya sun zo sun fahimci cewa wannan siyasar ta kudi ba ta ci.” Sabon-shigan ya soki halin 'yan siyasa.
A cewarsa matasa sun gaji da karbar N5, 000 ko N2, 000 domin a saye kuri’arsu a lokacin yin zabe ya ce yanzu lokaci ya yi da abubuwa za su sauya a kasar nan.
KU KARANTA: Mutane za su zabi APC a 2023 - Gwamna Uzodinma
Mista Ohuabunwa ya ce ya na goyon bayan mutumin Kudu maso gabas ya zama shugaban kasa, amma ya ce shi zai yi takarar ne domin ya cancanci ya yi mulki.
“Mutane su na canza jam’iyya farat daya, ba tare da sun tuntubi talakawansu ba, kuma a rika yi masu tafi, ana zabensu, jama’a babu akida, ni ba haka na ke ba.”
A jihar Kwara, kun ji an lakadawa shugaban jam’iyya dukan tsiya, yayin da ma’ajin APC na jihar yanzu ya ke kwance rai hannun Allah, kuma an karbe masa mota.
Shugaban riko na jam’iyyar APC a Kwara, Bashir Bolarinwa ya ce tsagerun da aka yi haya ne su ka yi wa mutanen bangarensa a jam’iyyar APC rugu-rugu a garin Ilorin.
Tun ba yau ba ana ta samun sabani tsakanin Bashir Bolarinwa da mutanen gwamnan jihar Kwara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng