Ta’addanci ne ba Tsageranci ba, Gumi ya yi magana bayan ya hadu da ‘Yan bindigan Zamfara

Ta’addanci ne ba Tsageranci ba, Gumi ya yi magana bayan ya hadu da ‘Yan bindigan Zamfara

- Dr. Ahmed Mahmoud Gumi ya ziyarci sansanin ‘Yan bindiga a Zamfara

- Malamin musuluncin ya yi magana bayan ya ga abubuwa da idanunsa

- Shehin ya ce Arewa na fama da matsalar ta’addanci ne ba tsageranci ba

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Ahmed Mahmoud Gumi ya bada labarin tafiyar da ya yi zuwa sansanin wasu ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Ganin yadda ake fama da matsalar rashin tsaro a Arewa maso yammacin Najeriya, babban malamin ya shiga inda ‘yan bindiga su ke, ya na lallabarsu.

Da yake yi wa gwamnan Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, bayanin abin da ya gani, Malamin ya bayyana cewa tsagerun ‘yan bindigan sun zama ‘yan ta’adda.

Jaridar Daily Trust ta ce Dr. Ahmed Mahmoud Gumi ya bayyana haka ne ranar Alhamis, 4 ga watan Fubrairu, 2021, a gidan gwamnati da ke garin Gusau.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi mani alkawarin ajiye makamai - Gumi

Shehin yake cewa rashin kula ne ya jawo wadannan mutane su ka zama gawurtattun ‘yan ta’adda.

Babban malamin ya yi kira ga gwamnatoci a kowani mataki, su yi sulhu da wadannan mutane, a cewarsa za a shawo kan matsalar ne ta hanyar neman lalama.

“A mafi yawan sansanin da na ziyarta a Zamfara, na zo na fahimci cewa abin da yake faruwa ba komai ba ne, ta’addanci ne da tada-kafar baya.” Inji Gumi.

“Wasu su na da ra’ayin cewa a auka wa miyagun nan, a hallaka su, amma abin da mu ka fahimta shi ne, yawancinsu jahilai ne dake bukatar ilmi da wayar da kai”

KU KARANTA: Malamai su yi koyi da Gumi wajen yi wa 'yan bindiga wa'azi - Gwamna

Dr. Ahmad Gumi ya bayyana abin da ya gani da ya shiga inda ‘Yan bindiga su ke
Dr. Ahmad Abubakar Gumi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sheikh Gumi ya ce ‘yan bindigan su na ta’adi ne saboda yawan kai masu hari da ‘yan sa-kai su ke yi.

Kafin yanzu, idan za ku tuna, Ahmed Mahmoud Gumi ya ziyarci wasu ‘yan bindiga a yankin Abuja da Kaduna, inda ake fama satar mutane da kashe-kashe.

A watan da ya gabata, Dr. Ahmed Gumi, ya ziyarci wasu rugage masu hatsari a kan hanyar Kaduna zuwa birnin tarayya Abuja, ya yi masu wa'azin addini.

A ra'ayin Dr. Gumi, jahilci da duhun kai ne su ke addabar Fulanin da ke zaune a wadannan wurare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel