Sheikh Gumi ya ziyarci rugage masu hatsari domin yi wa fulani wa'azi akan haramcin garkuwa da mutane

Sheikh Gumi ya ziyarci rugage masu hatsari domin yi wa fulani wa'azi akan haramcin garkuwa da mutane

- Babban Malamin addinin Musulunci, Dakta Ahmad Gumi, ya ziyarci wasu rugage masu hatsari a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Sheikh Gumi ya gabatar da lakca ga al'ummar Fulani a rugage da ya ziyarta domin fadakar da su illolin da ke tattare da sace mutane

- A cewar Sheikh Gumi, jahilci da duhun kai sune manyan matsalolin da ke addabar Fulanin da ke zaune a rugage

Sheikh Dakta Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ziyarci wasu rugagen Fulani da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Daily Trust ta rawaito cewa rugagen da Babban Malamin ya ziyarta sun kasance tamkar tarko wurin matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Yayin da yake gabatar da jawabi a gaban dumbin al'ummar Fulani a garin Jere, Sheikh Gumi ya bayyana damuwarsa a kan yadda hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama abar tsoro saboda rashin tsaro.

Sheikh Gumi ya nuna takaicinsa akan yadda duhun jahilci ya lullube kwakwalwar Fulanin da suke garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

KARANTA: 'Yan bindiga sun harbe wani limami a Kaduna saboda yawan sukarsu a hudubarsa

A cewarsa, bawa irin wadannan Fulani ilimin addini ko na zamani shine kadai mafita daga kangin jahilcin da ya jefasu cikin irin mummunar rayuwa.

Sheikh Gumi ya ziyarci rugage masu hatsari domin yi wa fulani wa'azi akan haramcin garkuwa da mutane
Sheikh Gumi ya ziyarci rugage masu hatsari domin yi wa fulani wa'azi akan haramcin garkuwa da mutane @Daily_trust
Asali: Twitter

Kazalika, ya dauki alkawarin cewa gidauniyarsa, duk da bata da karfi, zata gina makarantu guda biyu domin ilimintar da Fulani

Ya kara da cewa za'a kara zabar wasu daga cikin Fulanin domin basu horon da ilimin da zasu ke koyar da sauran Fulani 'yan uwansu.

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

Gumi ya bayyana cewa za'a kafa wani kwamiti da Fulani zasu ke shigar da korafinsu idan an yi musu wani rashin adalci domin nema musu hakkinsu.

A karshe, Sheikh Gumi ya rabawa al'ummar Fulanin wasu litattafai da zasu taimaka musu wajen sanin addini.

Daga cikin tawagar Sheik Gumi akwai Dakta Sulaiman Mahmud, babban limamin Masallacin Sultan Bello, jami'an tsaro, da wakilan kungiyoyin Malamai da dalibai.

Legit.ng ta rawaito cewa Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 23.

Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da Sauda Amina-Ayotebi.

Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel