'Yan bindiga sunyi alkawarin ajiye makamai bayan Gumi ya bi su garuruwansu ya musu wa'azi

'Yan bindiga sunyi alkawarin ajiye makamai bayan Gumi ya bi su garuruwansu ya musu wa'azi

- Tattaunawar Gumi da yan bindiga ya takaita yawan garkuwa da mutane a Jihar Kaduna

- Gumi ya shaida cewa yan bindigar sun tuba kuma sun bukaci a samar da kayayyakin more rayuwa a yankunan su sannan a daina bibiyar su

- Ya kara da cewa alkanta fulani da ta'addanci rashin adalci ne, saboda kaso 10 ne kadai suke da alaka da ta'addancin

Shugabannin yan bindiga a yankin Kidandan a karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna a ranar Talata sun bukaci za su tuba bayan tattaunawa da Dr Ahmad Gumi, Daily Trust ta ruwaito.

Dr Gumi wanda tun a farkon watan nan ya hada gangamin yawon Da'awa a yankunan da ta'addanci yayi kamari.

'Yan bindiga sunyi alkawarin ajiye makamai bayan Gumi ya bi su garuruwansu ya musu wa'azi
'Yan bindiga sunyi alkawarin ajiye makamai bayan Gumi ya bi su garuruwansu ya musu wa'azi. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam

A satin farko na Janairun 2021, malamin ya ziyarci kauyukan Fulani da ke hanyar Kaduna-Abuja, inda garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta'addanci ya fi kamari.

Daga bisani ya ziyarci Gamabira a karamar hukumar Soba kafin ya ziyarci Kidandan a karamar hukumar Giwa ranar Talata.

Malamin addinin musuluncin ya bayyana irin tulin jahilci a tsakanin Fulanin ya kuma tabbatar da cewa zai bada iya taimakon da zai bayar na karatun addinin musulunci.

A Kindandan ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito cewa shugabannin Fulani da kwamandojin yan ta'adda, mata da kananan yara, da shugabannin makiyaya na Miyetti Allah (MACBAN) sun sami hallatar da'awar.

KU KARANTA: 'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria

Gumi, wanda ya samu kariyar kwamishinan yan sanda na Jihar Kaduna, Umar Muri da jami'an sa, ya ce kwamandojin yan bindigar sun tuba tare da sakawa gwamnati sharadin samar musu da kayayyakin more rayuwa kuma jami'an tsaro su daina bibiyar su ko kama su.

Dr Gumi ya ce rashin adalci ne kiran su yan bindiga, ya kuma kara da cewa kaso 10 ne kadai na Fulani ke da alaka da ta'addanci.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel