Kuyi koyi da Gumi wajen yi wa yan bindiga da'awah, Matawalle ga malaman Zamfara

Kuyi koyi da Gumi wajen yi wa yan bindiga da'awah, Matawalle ga malaman Zamfara

- Gwamna Bello Matawalle ya yi kira ga malaman jihar a kan suyi koyi da Sheikh Gumi

- Babban malamin mazaunin Kaduna dai yana bi dazuka yana yi wa yan bindiga da'awar shiriya

- Matawalle ya kuma ce Sheikh Gumi ya fada masa cewa zai so wannan shiri nasa na yin wa'azi ya kai har jihar Zamfara

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya kalubalanci malaman addini a jihar, da su yi koyi da shahararren malamin nan na Kaduna, Sheik Ahmad Mahmud Gumi wajen yi wa yan ta’adda wa’azin shiriya.

Ziyarar da ya kai wasu dazuka masu hatsari ya yi sanadiyar da wasu shugabannin yan bindigan suka yi alkawarin tuba daga ayyukan ta’addanci.

Da yake magana kan ci gaban, Gwamna Bello Matawalle a taron gaggawa na masu ruwa da tsaki kan gina zaman lafiya a jihar tare malamai, sarakuna da shugabannin tsaro, ya ce Sheik Gumi ya kira shi sannan ya fada masa cewa zai so wanza da wannan kudiri har zuwa Zamfara.

Kuyi koyi da Gumi wajen yi wa yan bindiga da'awah, Matawalle ga malaman Zamfara
Kuyi koyi da Gumi wajen yi wa yan bindiga da'awah, Matawalle ga malaman Zamfara Hoto: BBC.com
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano Muhammad Sanusi I rasuwa

Ya nemi hakan ne kasancewarsa dan asalin jihar da son wanzar da zaman lafiya a jihar.

“Muna da malamanmu kuma ina ganin za su iya yin haka kuma ina bukatarsu da su tsara dabara kan yadda za a cimma haka. Muna kishirwar zaman lafiya a jihar nan.

“Akwai lokacin da na kira malamin nan na Gusau, Sheik Umar Kanoma da daddare don tattaunawa da wasu tubabbun yan bindiga sannan suka amince da ajiye makamansu kuma yanzu suna rayuwarsu na daban,” in ji shi.

A cikin haka, kwamishinan yan sanda na jihar, Mista Abutu Yaro ya ce malaman na iya taimakawa a wannan yanayi yayinda ya lamuncewa shirin sassanci na Gwamna Bello Matawalle.

Yaro ya ce malamai na iya farawa imma daga karamar hukuma zuwa wata ko kuma daga masarauta guda zuwa wata, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi zanga-zanga a Akure kan umurnin da Akeredolu ya baiwa makiyaya na ficewa daga jihar

Ya yi alkawarin cewa rundunar yan sandan jihar za ta kasance a shirye domin tallafa masu wajen cimma wannan manufa ta alkhairi.

A baya mun ji cewa babban Malami Sheikh Ahmad Gumi ya sanar da dalilinsa na shiga daji wa'azi.

Ya ce yin hakan yana da alaka da lamarin garkuwa da mutane da yayi yawa a kasar nan.

A cewarsa, akwai bukatar a koyar da su addini domin su gane abinda suke ba addini bane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng