COVID-19: Gwamnatin Kogi ta yi barazanar maka NCDC da PTF a kotu

COVID-19: Gwamnatin Kogi ta yi barazanar maka NCDC da PTF a kotu

- Gwamnatin jihar Kogi ta ci alwashin maka gwamnatin tarayya a kotu kan zargin bata jihar

- Gwamnatin Kogi ta bayyana cewa NCDC da PTF na kokarin sanya wa mutane tsoron jihar

- Jihar ta siffanta zancen NCDC da PTF a matsayin yunkurin gurgunta tattalin arzikin jihar

Dangantaka mai tsanani tsakanin Kogi da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa / kwamitin shugaban kasa (PTF) akan COVID-19 na kara munana tare da gwamnatin jihar a yanzu da ke barazanar shigar da karar gwamnatin tarayya kotu.

Kingsley Fanwo, Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Kogi ya bayyana aniyar gwamnatin jihar na kai karar PTF-COVID-19 a Lokoja ranar Laraba kan abin da ya bayyana a matsayin wani yunkurin durkusar da jihar da kuma jefa ‘yan kasa cikin fargaba.

Gwamnatin Jihar ta zargi PTF-COVID-19 da gazawa a kokarin da ta yi a baya na shigo da Covid-19 zuwa Kogi kuma saboda haka, yanzu ta koma haifar da tashin hankali, PM News ta ruwaito.

KU KARANTA: Buhari ya amince da bai wa sabbin jami’o’i 20 masu zaman kansu lasisi

COVID-19: Gwamnatin Kogi ta yi barazanar maka NCDC da PTF a kotu
COVID-19: Gwamnatin Kogi ta yi barazanar maka NCDC da PTF a kotu Hoto: Premium Times
Source: Facebook

Fanwo yana mayar da martani ne ga bayanin ranar Litinin na Kogi a matsayin jiha mai matukar hadari da ya kamata matafiya su kaurace mata saboda halin rashin tsari da gwamnatin jihar ta nuna game da cutar COVID-19 da PTF ta yi.

Amma Fanwo ya ce ikirarin da NCDC da Task Force suka yi shi ne don lalata jihar ta hanyar tsoratar da masu saka hannun jari a karshe kuma, a gurgunta tattalin arzikin Kogi.

“Mun yi imani sosai cewa aniyarsu ita ce tabbatar da masu zuba jari suna tsoron zuwa jihar. Duk da alkalumman da suka bayar na karya, Kogi ta zama makasudin saka hannun jarin Nijeriya a rubu'in karshe na 2020.

"Sun ji kunya kuma babbar hanyar da za su iya mayar da martani ita ce samar da hoto game da rikicin kiwon lafiya a jihar."

KU KARANTA: Ni nayi wuff da mijina: Aisha Yesufu tace 'yan mata su daina jiran samari

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da wasu jami'ai 2,000 na COVID-19 domin fadakarwa tare da aiwatar da ladabi kan tsaro a jihar, PM News ta ruwaito.

Ganduje ya ce a lokacin kaddamarwar a Kano ranar Lahadi cewa akwai bukatar a magance COVID-19 da dukkan kokari da za a iya yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel