Shahararren malamin Musulunci Sheikh Gumi ya yi babban hasashe kan fashi a arewa
- Ta’addanci zai zo karshe a arewa kwanan nan, a cewar Sheikh Ahmad Gumi
- Shahararren malamin Musuluncin ya kuma nuna yakinin cewa rikicin makiyaya da manoma zai zama tarihi
- Gumi da tawagarsa sun je jihar Zamfara don tattaunawa da tubabbun yan bindiga da kuma wasu manyan malamai
Shahararren malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya nuna tabbacin cewa fashi da makami da garkuwa da mutane za su zama tarihi a jihar Zamfara da arewa.
Gumi ya bayar da tabbacin ne a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairu, a yayinda ya ziyarci jihar Zamfara kan batun tattaunawa da yan bindigar da ke muradin ajiye makamansu.
Malamin ya ce zaman lafiya zai dawo arewa da Naeriya, inda ya kara da cewa ana kokari don samun mafita mai dorewa kan rikicin manoma da makiyaya, TVC News ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Jami’ar Al-Qalam da wasu jami’o’i masu zaman kansu guda 98 a Nigeria
Gumi da tawagarsa na rangadi a wasu jihohin arewa a wani yunkuri da ake ganin zai taimakawa gwamnati wajen kawo karsgen ta’addanci da fashi da makami.
A ziyarar da ya kai Zamfara, ya samu tarba daga kwamishinan tsaro da sauran mambobin majalisar zartarwa ta jihar.
Legit.ng ta lura cewa Gumi, babban limami a masallacin Juma’a ta Sultan Bello da ke Kaduna, yana da kima da babban matsayi a arewa.
Tawagarsa, da rakiyar wasu malaman, sun ziyarci Rugar Maradun wanda gwamnatin Gwamna Bello Matawalle ta kafa don magance rikicin makiyaya da manoma a jihar.
KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki: Yan bindiga sun halaka mutane 13 a jihar Katsina
A baya mun ji cewa Malami, Sheikh Abubakar Gumi ya yi wata ganawa da shugabannin 'yan fashi a Zamfara don fahimtar juna da magance rashin tsaro a jihar.
Malamin, a kokarinsa na da'awar wanzar da zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya, ya kan ziyarci wuraren da 'yan fashin suke domin tattaunawa da fahimtar juna.
Malamin yana shiga dazuka inda 'yan bindigan suke domin yi musu nasiha wanda hakan a baya ya jawo tuban wasu daga cikin 'yan bindigan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng