Cikin Hotuna: Sheikh Abubakar Gumi ya gana da shugabannin 'yan bindiga a Zamfara
- Sheikh Abubakar Gumi ya ziyarci wani wajen 'yan bindiga domin tattaunawa dasu
- Hotuna sun watsu a kafafen sada zumunta yana zaune tare da 'yan bindigan
- Rahotanni sun bayyana cewa ya ziyarce su ne domin tattaunawa da shugabannin 'yan bindigan
Malami, Sheikh Abubakar Gumi ya yi wata ganawa da shugabannin 'yan fashi a Zamfara don fahimtar juna da magance rashin tsaro a jihar.
Malamin, a kokarinsa na da'awar wanzar da zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya, ya kan ziyarci wuraren da 'yan fashin suke domin tattaunawa da fahimtar juna.
Malamin yana shiga dazuka inda 'yan bindigan suke domin yi musu nasiha wanda hakan a baya ya jawo tuban wasu daga cikin 'yan bindigan.
Kalli hotunan:
KU KARANTA: 'Yan fansho a jihar Gombe sun yi zanga-zanga a gidan gwamnati
KU KARANTA: Buhari ya amince da bai wa sabbin jami’o’i 20 masu zaman kansu lasisi
A wani labarin daban, Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake ankarar da ‘yan Najeriya game da shirin da wasu mutane da kungiyoyi ke yi na haifar da rikicin kabilanci da addini a wasu sassan kasar.
Hukumar DSS a watan Junairu ta yi bayanin cewa wasu mutane suna aiki tare da mutanen waje don tayar da rikicin addini a fadin kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng