Abun bakin ciki: Yan bindiga sun halaka mutane 13 a jihar Katsina
- Mahara sun kai farmaki a garin Sabuwa na karamar hukumar Sabuwa, Jihar Katsina, inda suka kashe mutum 13 tare da raunata wasu
- Harin ya kasance na ramuwar gayya bayan kwace shanu da ’yan bindigar suka yi daga hannun wasu matasa da ke dibar yashi da su amma matasan suka kwato shanun
- An kai harin ne a ranar Talata, 2 ga watan Fabrairu
Yan bindiga sun kai hari garin Sabuwa da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, sun kashe mutane 13 da kuma jikkata wasu da dama.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin garin ya bayyana cewa harin ya biyo baya ne bayan yan bindigar sun karbi shanaye daga yaran da ke amfani da su wajen dibar yashi a amalanke a wajen garin.
Ya ce wannan ya yi sanadiyar da aka yi arangama da mazauna garin a kokarinsu na kwato shanayen.
KU KARANTA KUMA: Tsohuwar da bata samu haihuwa ba ta ce ita da kanta ta nema wa mijinta sabuwar mata
Sun yi nasarar kwato dabbobi da dama amma sai yan bindigar suka sake haduwa suka fara harbi ba kakkautawa, in ji shi.
“Matasan sun kai kara bayan kwace shanun daga hannunsu, sai samarin suka gayyato abokansu suka kwato su daga hannun ’yan bindigar.
“Abun bakin ciki, sai ’yan bindigar suka gayyato abokansu sama da 100 suka rika harbin duk wanda suka gani a kauyen,” in ji wani mazaunin yankin.
Ya ce maharan sun kai mamaya garin da misalin karfe 5:30 na daren ranar Talata, sannan an binne biyu daga cikin mutanen a wannan rana yayinda aka binne sauran 11 a ranar Laraba bayan an yi masu sallah a masallacin Jumata da ke Sabuwa.
KU KARANTA KUMA: Yaki da ta’addanci: El-Rufai ya ce sabbin shugabannin tsaro za su yi nasara
A wani labarin, mun ji cewa a ƙalla mahara uku yan sanda suka aika lahira cikin daren Talata a ƙaramar hukumar Ɗanmusa dake jihar Katsina.
Maharan waɗanda adadinsu ya haura hamsin, sun kutsa ƙauyukan Unguwar Ɓera da Tasha Mangoro cikin wannan daren, daga bisani mazauna ƙauyukan suka nemi agaji daga jami'an tsaro.
Tawagar jami'an rundunar 'yan sanda ta kaddamar da harin kwanton bauna tare da tarfa tawagar 'yan bindigar a wani wuri da ke tsakanin kauyukan Mara da Tashar Gajere.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng