Abin da ya sa Na’Abba, Utomi, Sonaiya, da Moghalu za su kafa wata Jam’iyya
- Wasu ‘Yan siyasa sun shirya kafa sabuwar Jam’iyya da za ta nemi mulki
- Ghali Na’ Abba, Baba-Ahmed, da Agbakoba ne kan gaba a wannan tafiyar
- ‘Yan kungiyar National Consultative Front za su narke a cikin jam’iyyar
A watan Maris mai zuwa ne za a sanar da bayyanar wata sabuwar jam’iyya a Najeriya.
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Fubrairu, 2021 cewa wasu fitattun ‘yan siyasar kasar nan sun hadu, za su kafa jam’iyya.
Daga cikin wadanda ke kan gaba wajen wannan tafiya akwai tsohon shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba da Olisa Agbakoba SAN.
Tsofaffin ‘yan takarar shugaban kasa irinsu Farfesa Pat Utomi, Farfesa Remi Sonaiya, da Dr. Kingsley Moghalu su na cikin wannan sabuwar tafiya.
KU KARANTA: Rikicin PDP ya ki cinyewa, Sanatar Ekiti ta kai Fayose kotun koli
Wannan jam’iyya da za a kafa ta na kunshe da irinsu Dr. Hakeem Baba-Ahmed, Dr. Obadiah Mailafia, Issa Aremu, da kuma Farfesa Chidi Odinkalu.
Haka zalika akwai Precious Elekima, Ezekiel Nya-Etok, Tanko Yunusa da Peter Ameh.
Da su ke magana a karkashin lemar National Consultative Front, NCF a birnin Abuja a jiya, ‘yan siyasar sun ce gazawar shugabanni ta sa su kafa tafiyarsu.
A cewarsu, masu rike da mulki su na neman kai Najeriya kasa don haka su ka daura damarar yaki da matsalar tattali, garkuwa da mutane da tada-zaune-tsaye.
KU KARANTA: 'Yan siyasan da ke harin kujerar Shugaban kasa a 2023
‘Ya ‘yan wannan kungiyar sun ga bukatar su kafa jam’iyyar siyasa da za ta ba su mulki domin cin ma manufar su na kawo karshen matsalolin da ake fama da su.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fada wa matasa irin hanyar da za su bi domin su yi caraf da shugabancin Najeriya daga hannun shugabannin kasar.
Olusegun Obasanjo ya ce tsofaffin da ke rike da kasar nan ba za su ba matasa mulki a bagas ba.
Wannan ya sa dattijon ya yi kira ga masu tasowan da su yi amfani da damarsu, su hana wadanda ke rike da madafan iko sakat, domin mulkin kasar ya dawo hannunsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng