Rijista: An tashi baran-baran ba shiri baya rikice ya barke yayin taron shugabannin APC

Rijista: An tashi baran-baran ba shiri baya rikice ya barke yayin taron shugabannin APC

- Rikici ya barke a tsakanin jagororin APC reshen jihar Kwara akan aikin sabunta rijistar zama mamba

- Wasu matasa sun yi yunkurin hana shugaban riko na jam'iyyar APC da shugabar mata su shiga wurin taron jam'iyya

- Rahotanni sun bayyana cewa an farfasa gilashin motar shugabar mata ta jam'iyyar tare da yin awon gaba da wasu kaya mallakinta

Rikici ya barke a jihar Kwara a ranar Laraba, yayin da jam'iyyar APC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar kan batun sabunta katin shaidar zama mamba a jam'iyyar kamar yadda uwar jam'iyyar ta kasa ta aike da kwamiti a jihar.

Rikicin ya fara ne tun bayan da wasu matasan APC suka hana shugaban riko na jam'iyyar a jihar Hon Bashir Bolarinwa, shugabar mata ta jam'iyyar, Ramat Laide Alake da magoya bayansu shiga cikin dakin taron, da ke kusa da gidan gwamnatin jihar.

Rahotan The Nation bayyana cewa an tilasta shugaban kwamitin yin sabuwar rejista da sabunta wa, Sanata John Danboyi da sauran mambobin kwamitin barin dakin taron cikin gaggawa.

KARANTA: An kama matasan da ke dillancin hotunan tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo

Haka zalika, rahotanni sun bayyana cewa an farfasa gilashin motar shugabar mata ta jam'iyyar, yayin da aka yi awon gaba da wasu kaya mallakin ta.

Rijista: An tashi baran-baran ba shiri baya rikice ya barke yayin taron shugabannin APC
Rijista: An tashi baran-baran ba shiri baya rikice ya barke yayin taron shugabannin APC
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Abdulrahman AbdulRazaq ba ya dakin taron lokacin da wannan hatsaniya ta kaure.

Gwamnan ya ƙaddamar da bude sabuwar rejista da sabunta wa a gundumar Idi Igba, karamar hukumar Ilorin ta Yamma da ke jihar.

KARANTA: ASP: Buhari ya bullo da sabon tsarin ilimi don 'ya'yan talakawa

Jim kaɗan bayan kaddamar da rejistar, Gwamna AbdulRazaq ya ce akwai bukatar buda rassan yin rejistar jam'iyyar a sassan jihar.

Ya ce shirin yin rijistar na da muhimmanci la'akari da cewa jam'iyyar na ci gaba da haɓaka, sakamakon ayyukan raya al'umma da jam'iyyar ta gudanar a jihohi da ma kasar baki daya, don haka akwai bukatar sabunta rijistar wadanda suka yi tsayin daka har jam'iyyar ta samu nasara a zabukan baya da kuma yin rajista ga sabbin mambobi.

Legit.ng ta rawaio cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sanar da bullo da sabon shirin ASP don ilimantar da yara marasa galihu.

ASP sabon shirin gwamnatin Buhari ne da zai tabbatar da bayar da ilimi kyauta ga yara marasa galihu da basa zuwa makaranta

Shugaba Buhari ya bayyana cewa burin gwamnatinsa shine bayar da ilimi ga dukkan yaran da ke Nigeria

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel