Buhari ne Shugaban kasar farko da ba ya shiga hurumin NNPC inji Kaka Kyari

Buhari ne Shugaban kasar farko da ba ya shiga hurumin NNPC inji Kaka Kyari

- Mele Kolo Kyari ya ware Buhari a cikin duka Shugabannin da aka yi a Najeriya

- Shugaban kamfanin NNPC ya ce Shugaban Najeriyar ba ya yi masu katsalandan

- Kyari ya ce ba a taba ganin wannan a tarihin NNPC ba, kuma hakan ya taimaka

Shugaban kamfanin mai na kasa watau NNPC, Mallam Mele Kyari, ya ware Muhammadu Buhari a cikin shugabannin da aka yi, ya yabe shi.

A cewar Mallam Mele Kolo Kyari, Muhammadu Buhari ne shugaban kasar da aka yi wanda bai tsoma baki a cikin harkar gudanarwar kamfanin NNPC.

Vanguard ta ce Mele Kolo Kyari ya fitar da jawabi ne a ranar Talata, 2 ga watan Fubrairu, 2021, ta bakin shugaban hulda da jama’a na NNPC, Kennie Obateru.

Dr. Kennie Obateru ya ce shugabannin NNPC sun yi sa’a da su ka samu shugaban kasar da bai taba yi wa NNPC katsalandan a matsayinta na kamfani ba.

KU KARANTA: “Buhari bai yi abin da aka kawo shi ya yi ba” inji Bakare

Shugaban NNPC ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake jawabi a wajen wata lacca da aka gudanar a jami’ar Usman Danfodiyo da ke garin Sokoto.

Jaridar Vanguard ta ce an yi wa wannan laccar da aka yi take da ‘Navigating Energy Transition and the Imperatives of University-Industry Collaboration.”

“Abu ne da ba a taba gani ba a tarihi, kuma hakan ya taimaka mana wajen cin ma burinmu, musamman wajen habaka amfani da arzikin gas.” Inji Kyari.

Kyari ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika su rika amfani da fasahar zamani domin samar da arzikin mai da gas, wanda yake da tasiri ga tattalin arziki.

Buhari ne Shugaban kasar farko da ba ya shiga hurumin NNPC inji Kaka Kyari
Shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari Hoto: www.petrobarometer.thecable.ng
Asali: UGC

KI KARANTA: Yajin-aiki: Gwamnatin Tarayya ta gaza shawo kan Ma’aikatan Jami’a

Shugaban na NNPC ya kuma bayyana irin kokarin da su ka yi wajen harkar bincike, sannan ya ce kofa a bude take ga masana domin su ba kamfanin gudumuwa.

A jiya ne mu ka ji cewa wakilan gwamnatin tarayya za su koma kan teburin tattaunawa da shugabannin kwadago da ke wakiltar bangaren ma’aikata a Abuja.

Ministan kwadago, Chris Ngige ya ce sun sa ranar duba rahotonnin kudin shan wutar lantarki da farahin litar fetur, bayan binciken da kwamitoci su ka gabatar.

Hakan na zuwa ne bayan vwamnatin Muhammadu Buhari ta kara kudin litar mai da na wuta a 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng