Zamu iya gayyatar mayakan kasashen waje su lalata Najeriya, Jagoran 'yan ta'adda

Zamu iya gayyatar mayakan kasashen waje su lalata Najeriya, Jagoran 'yan ta'adda

- Shugaban kungiyar 'yan ta'adda a jihar Zamfara ya bayyana cewa zai iya gayyatar 'yan waje a lalata Najeriya

- Yayi wannan alwashine yayin tattaunawa da yayi da wani malamin addini dan jihar Kaduna

- Malamin, Sheikh Abubakar Gumi ya ziyarci wajen 'yan ta'addan domin tattauna yadda za a samar da zaman lafiya

Shugaban 'yan ta'addan da ke zaune a Zamfara, Turji, ya yi barazanar gayyatar mayaka 'yan kasashen waje don tayar da zaune tsaye a Najeriya, HumAngel ta ruwaito.

Wani shugaban ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Kachalla Turji, ya ce kungiyarsa na iya yin kira ga goyon bayan kasashen waje don yaki da dagula Najeriya.

An ji Turji a cikin wani faifan bidiyo da aka yada a kafar Facebook suna tattauna korafe-korafen da suka ci gaba da kashe-kashe, satar mutane da kungiyoyin masu satar shanu a yankin.

Ya yi magana ne kan asalin kokarin da gwamnati ke yi wanda ta raina karfin kungiyar tasa a taron da aka yi tsakanin Dakta Ahmad Abubakar Gumi, wani malamin addinin Islama na arewa mai tasiri kan mambobin kungiyar a ranar Talata.

KU KARANTA: Ni nayi wuff da mijina: Aisha Yesufu tace 'yan mata su daina jiran samari

Zamu iya gayyatar mayakan kasashen waje su lalata Najeriya, Jagoran 'yan ta'adda
Zamu iya gayyatar mayakan kasashen waje su lalata Najeriya, Jagoran 'yan ta'adda Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

Ganin yadda mayaka ke rike da bindigogi, Turji, sanye da kayan boye kamanni, ya fadawa malaman da Gumi ya jagoranta a kan aikin samar da zaman lafiya, cewa gwamnatin Najeriya bata cika alkawura ba.

Ya ce kungiyarsu ta halarci taron ne saboda malaman addinin Musulunci ne suka shirya shi.

Wani daga cikin 'yan bindigan yana rataye da RPG a yayin zaman, wanda ya gudana a yankin Shinkafi na jihar Zamfara, daya daga cikin jihohin arewa maso yamma, inda kungiyoyin ‘yan ta’adda ke ta addabar al’ummar yankin.

Ziyarar ta Gumi na daga cikin kokarinsa na samar da zaman lafiya da kuma wayar da kai ga al'ummomin Fulani da kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin Arewa maso Yamma.

Shehin malamin ya zagaya wurare daban-daban a cikin Zamfara, inda ya hada baki da jami’ai, shugabannin gargajiya da wadanda ba ‘yan jihar ba a kokarin da yake na bayar da gudummawa wajen kawo karshen rikici a jihar.

KU KARANTA: Buhari ya amince da bai wa sabbin jami’o’i 20 masu zaman kansu lasisi

A wani labarin, Malami, Sheikh Abubakar Gumi ya yi wata ganawa da shugabannin 'yan fashi a Zamfara don fahimtar juna da magance rashin tsaro a jihar.

Malamin, a kokarinsa na da'awar wanzar da zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya, ya kan ziyarci wuraren da 'yan fashin suke domin tattaunawa da fahimtar juna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel