Ni nayi wuff da mijina: Aisha Yesufu tace 'yan mata su daina jiran samari

Ni nayi wuff da mijina: Aisha Yesufu tace 'yan mata su daina jiran samari

- A kwanakin baya ne wata ‘yar gwagwarmaya Aisha Yesufu ta shawarci matan da shekarunsu bai su wuce 30 zuwa sama ba

- 'Yar gwagwarmayar ta ce su nemi maza su aure su maimakon su jira zuwansu

- Aisha ta bayyana cewa ita ta ga mijinta, ta ƙaunace shi, kuma ta tambaye shi ya aureta

Wata ‘yar fafutuka kare hakkin dan Adam a Najeriya Aisha Yesufu ta bayyana cewa ita ta jawo hankalin mijinta da kanta. Aisha ta fadi haka ne a wata hira da tayi da BBC News Pidgin.

Aisha uwa mai 'ya'ya biyu ta bayyana cewa ko yaushe tana bai wa mata shawara daga shekaru 30 zuwa sama da kada su jira har sai wani namiji ya zo ya latsa su kafin suyi aure.

A cewarta, mata suna zuwa wurin mazajen da suke so kuma suna neman aurensu.

KU KARANTA: Cikin Hotuna: Sheikh Abubakar Gumi ya gana da shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

Ni nayi wuff da mijina: Aisha Yesufu ta ce matan da ba su da aure su daina jiran samari
Ni nayi wuff da mijina: Aisha Yesufu ta ce matan da ba su da aure su daina jiran samari Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

Aisha tace:

"A kan shawarar da na ba 'yan mata ita ce su daina jiran wani mutum ya zo ya neme su.
"Kun fi shekaru 30 kuma za ku shiga shekarunku na 40 zuwa 50 kuma sai ku ce kuna jiran wani mutum ya zo ya nemi aurenku.
"Ta yaya hakan zai faru, babu matsala ko da kuwa kun girme shi, batun aure batun gaskiya ne, don haka, kar dai ku zauna ku jira duk wanda ya zo muku."

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: Buhari ya amince da bai wa sabbin jami’o’i 20 masu zaman kansu lasisi

A wani labarin, A cewar wasu masu yada ilimin Kimiyya, Fasaha, Injiniyanci da Lissafi (STEM), idan aka zo batun shiga STEM, alkaluman suna kan raguwa a Arewacin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Masu ba da shawara na STEM sun ce wannan raguwar za a iya danganta shi da dalilai da yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel