IGP Adamu da manyan jami'an 'yan sanda uku da zasu yi ritaya a mako mai zuwa

IGP Adamu da manyan jami'an 'yan sanda uku da zasu yi ritaya a mako mai zuwa

- Babban sifeton rundunar 'yan sanda tare da mataimakansa manya da kanana guda goma sha uku zasu yi ritaya

- Doka ta tanadi cewa jami'an dan sanda zai yi ritaya idan ya cika shekaru 60 a duniya ko kuma shekaru 35 yana aiki

- Bisa al'adar gwamnatin Nigeria, akan sanar da sabon IG kafin na kai ya sauka daga kan kujerar

A ranar Litinin ne ake sa ran cewa babban sifeton rundunar 'yan sandan Nigeria, IGP Mohammed Adamu, da dumbin wasu manyan jami'ai zasu yi ritaya.

Premium Times ta rawaito cewa IGP Adamu da sauran manyan jami'an zasu yi ritaya ne saboda sun cinye wa'adin lokacinsu na aiki.

IGP Adamu, wanda ya shiga aikin dan sanda a ranar 1 ga watan Fabarairu na shekarar 1986, zai yi ritaya sakamakon cika shekaru 35 yana aiki.

A watan Janairu na shekarar 2019 tsohon shugaban IGP Ibrahim Idris ya mika ragamar tafiyar da al'amuran rundunar 'yan sanda ga IGP Adamu.

Bayan shi kansa IGP Adamu, akwai manyan mataimakansa (DIGs) guda uku da wasu sauran mataimakansa (AIG) guda goma da zasu yi ritaya daga aiki.

IGP Adamu da manyan jami'an 'yan sanda uku da zasu yi ritaya a mako mai zuwa
IGP Adamu da manyan jami'an 'yan sanda uku da zasu yi ritaya a mako mai zuwa
Asali: UGC

Manyan mataimakan sun hada da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Lamurde, Aminchi Baraya, da Nkpa Inakwu.

Sauran mataimakan (AIGs) sun hada da; Nkereuwem Akpan, Olafimihan Adeoye, Agunbiade Labore, Undie Adie, Olugbenga Adeyanju, Asuquo Amba, Mohammed Mustapha, Jonah Jackson, Olushola Babajide, da Yunana Babas.

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan sabuwar dokar da zata tilasta duk wani dan sanda yin ritaya idan ya kai shekaru 60 a duniya ko kuma shekaru 35 yana aiki.

Bisa al'adar gwamnati, akan sanar da sabon IGP yayin da ya rage saura kwanaki na kai ya sauka.

Sai dai, har yanzu babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa dangane da batun nadin sabon IGP duk saura sa'o'i na kai ya yi murabus.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel