Duk da rade-radin maye gurbinsa, IGP ya tarba shugaba Buhari bayan sauka Abuja daga Daura

Duk da rade-radin maye gurbinsa, IGP ya tarba shugaba Buhari bayan sauka Abuja daga Daura

- Mutane sun yi ta cece-kuce tun ranar Litinin akan yadda wa'adin IGP Mohammed Adamu ya kare, sakamakon cikarsa shekaru 60

- A ranar Talata aka ga Mohammed Adamu a filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja ya je tarbar Buhari daga tafiyar da yayi zuwa Katsina

- Dama ana sa ran idan Buhari ya dawo daga tafiyar ranar Talata, ranar Laraba zai sanar da sabon IGP da zai maye gurbin Mohammed Adamu

Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a ranar Talata lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Katsina.

Ya kamata Adamu ya sauka daga kujerarsa a ranar Litinin, saboda cikarsa shekaru 60, The Cable ta wallafa.

A ranar Talata ne aka ga IGP din ya je tarbar Buhari yayin dawowarsa daga tafiyar da yayi zuwa Katsina.

Duk da rade-radin maye gurbinsa, IGP ya tarba shugaba Buhari bayan sauka Abuja daga Daura
Duk da rade-radin maye gurbinsa, IGP ya tarba shugaba Buhari bayan sauka Abuja daga Daura. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: PTF ta ce Kogi jiha ce mai tarin hatsari, ta ja kunnen 'yan Najeriya a kan ziyara

Duk da dai an yi ta samun labarai iri-iri akan wanda zai gaji kujerar Adamu, Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya bayyana cewa za a zabi magajinsa ne ba tare da an duba bangaranci ba.

"Idan aka ce za a bi ta bangaranci wurin zaben shugabannin tsaro to tabbas za a zabi akalla mutane 250 daga kowanne yanki. Don kowa yana da nashi salon gudanar da mulkin," kamar yadda Shehu yace a wata tattaunawa da Channels Television tayi dashi a ranar Litinin.

A cewar Shehu, nagarta za a bi da cancanta ba wai bangaranci da kabilanci ba.

KU KARANTA: Matashi ya sheka lahira saboda 'tsabar gamsuwa' bayan kwana da budurwa a otal

A wani labari na daban, wata kotun tafi da gidanka a Abuja ta bada umarnin rufe kasuwar Wuse da ke Zone 5 saboda take dokokin dakile yaduwar cutar korona a kasuwar, The Cable ta wallafa hakan.

An rufe kasuwar UTC da rukunin shagunan Murg da ke yanki na 10 a Garki duk bayan umarnin kotun.

Kwamitin tabbatar da bin dokar korona ta Abuja wacce ta ziyarci kasuwar a ranar Litinin ta bayyana yadda ta samu babu na'urar gwada dumin jiki, ba a amfani da takunkumin fuska da kuma abubuwan wanke hannu a kasuwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel